✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

3 ga Nuwamba za a fara gasar Firimiya ta Najeriya

Hukumar Shirya Gasar  Rukunin Kwallon Kafa ta Kasa (LMC) ta  tsayar da ranar da za a fara karkar wasan  Rukunin Firimiya ta bana (2019/2020). Sanarwar…

Hukumar Shirya Gasar  Rukunin Kwallon Kafa ta Kasa (LMC) ta  tsayar da ranar da za a fara karkar wasan  Rukunin Firimiya ta bana (2019/2020). Sanarwar ta biyo bayan zaman da hukumar ta yi a ranar Litinin da ta gabata tare da shugabannin kungiyoyin kwallon kafa 20 da ake sa ran za su fafata a wasannin na kakar ta bana.

Shugaban Hukumar LMC, Malam Shehu Dikko ya yi wa shugabannin kungiyoyin bayani dangane da halin da gasar take ciki a yanzu musamman wadanda suka shafi yadda za a habaka kasuwanci da yadda za a kau da kalubalen da gasar take fuskanta.

Tun da farko an gabatar da bukatar fara wasannin ne cikin kwanaki biyu mabambanta wato ko dai a fara a ranar 20 ga Oktoba ko ranar 27 Oktoba,  inda daga bisani bayan an tattauna aka tsayar da ranar 3 ga watan Nuwamban bana 2019 a matsayin ranar da za a fara gasar.

Batutuwan da mahalarta taron suka tattauna sun hada da gabatar da godiyarsu ga Ministan Wasanni da Matasa Mista Sunday Dare, ganin  yadda yake bada goyon baya ga Hukumar NPFL da yadda yake kokarin kawar da wasu daga cikin kalubalen da hukumar take fuskanta.

Daga karshe mahalarta taron sun shaida yadda aka gudanar da rabon rukuni-rukunin wasannin kakar bana wacce ake sanya ran za ta kare a 31 ga watan Mayu na badi.