A ranar 1 ga Janairun nan ne Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi ga jama’ar kasa don murnar shiga sabuwar shekara a karo na farko.
Jim kadan bayan kammala jawabin ne kuma, sai ya rattaba hannu a kan Kasafin Kudin 2024.
- Muna ƙoƙarin kakkaɓe matsalar tsaro amma har yanzu ba mu yi nasara ba — Tinubu
- Mun soke lasisin duk makarantu masu zaman kansu — Gwamnatin Yobe
Shugaban ya rattaba hannun a kasafin Naira tiriliyan 28.87 bayan Majalisar Dokoki ta Kasa ta duba, tare da yin wasu gyare-gyare, sannan ta amice da kasafin.
Aminiya ta jiyo cewa Majalisar Dokokin ta kara sama da Naira tiriliyan a kan asalin kasafin da Bangaren Zantarwa ya aika mata.
Wannan shi ne Kasafin Kudi na farko da Shugaba Tinubu ya yi, kasancewar ya gaji ragowar kasafin bara, wanda tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi.
Sai dai jawabin na Shugaban Kasar da kuma kasafin kudin sun jawo muhawara a tsakanin al’ummar kasa.
A jawabin Shugaban Kasar ya bayyana cewa: “Za mu yi aiki tukuru domin tabbatar da ganin duk dan Nijeriya ya amfana da wannan gwamnati. Har marasa karfi duk babu wanda za a bari a baya.
“A karkashin hakan za mu gabatar da sabon tsarin albashi mafi karanci ga ma’aikata a bana.
“Kuma ba zan daga kafa ga duk wanda na bai wa mukami ba, idan bai yi aiki yadda ya dace ba.
“A 2024 za mu kara hobbasa wajen soma tace danyen mai a Matatar Mai ta Fatakwal da ta Dangote wadanda za su soma aiki gadan-gadan,” in ji shi.
Ya kara da cewa: “Mun shirya domin farfado da dukan fannoni, bayan hanyoyin farfado da tattalin arzikin kasa da muka samar cikin wata bakwai a 2023.
“Domin tabbatar da samar da abinci da tsaro, za mu gaggauta noma hekta 500,000 na masara da shinkafa da alkama da dawa da sauran hatsi.
“Duk da cewa ba za mu iya bugun kirjin cewa mun shawo kan duk matsalolin tsaro ba, amma muna aiki tukuru domin samar da zaman lafiya a gidajenmu da wuraren aiki da duk lungu da sakon kasar nan.”
Shugaba Tinubu ya kuma ce, “Gwamnatinmu ta fahimci babu wani ci gaba da za a samu muddin wutar lantarki ba ta wadata ba.
“Muna shirin kaddamar da wasu ayyukan samar da wutar lantarki da inganta tashoshin samar da wutar a fadin kasar nan.
“Ni da Shugaban Gwamnatin Jamus, Olaf Schlz mun kulla yarjejeniyar yin aiki cikin gaggawa domin kammala aikin da Kamfanin Siemens ke yi, wanda zai samar da wutar lantarki ga gidaje da wuraren kasuwanci wanda aka soma a 2018.
“A 2024 za mu yi hobbasa wajen ganin duk wasu batutuwa na kudi da haraji da suka kamata a sanya su bisa tsari, an yi su yadda ya dace saboda kada a samu koma baya.
“Zan soke duk abin da zai kawo tarnaki ga kasuwanci a kasar, ko zai hana Nijeriya zama cibiyar kasuwanci ga masu son zuba jari na cikin gida da na kasashen waje.”
Shugaba Tinubu ya ce, “A duk wata tafiya da na yi zuwa kasashen waje, sakon da nake bayarwa shi ne Nijeriya a shirye take domin yin kasuwanci da kowa.”
“Mun kaddamar da noman rani a filin da ya kai hekta 120,000 a Jihar Jigawa a watan Nuwamban 2023, a karkashin shirinmu na bunkasa noman alkama,” in ji shi.
Yadda za a ci moriyar kasafin kudin bana — Masana
Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’ntu da Ayyukan Gona ta Jihar Legas (LCCI), ta shawarci Shugaba Tinubu ya jawo musu zuba jari a bangaren makamashi, wanda a cewarta hakan zai bunkasa tattalin arzikin kasar nan.
Darakta Janar na kungiyar, Chinyere Almona ce ta bayyana haka a wata sanarwa, inda a ciki ta ce, “Akwai bukatar a gaggauta inganta bangaren makamashi.”
Ta kara da cewa duk wani kokari da za a yi wajen bunkasa bangaren noma, ba za a samu nasara ba matukar ba a samar da tsaro ba.
Ta ce akwai bukatar a inganta aikin ’yan sanda domin fadadawa da gyara aikinsu domin samar da tsaro a lungu da sakon kasar nan.
Ta kara da cewa duk da cewa janye tallafin man fetur mataki ne mai kyau, rage radadin da mutanen kasar suka shiga yana da matukar muhimmanci.
A bangaren Darakta Janar na Kungiyar Masu Daukar Aiki ta Nijeriya (NECA), Mista Oyerinde Adewale-Smart ya ce akwai bukatar a rage kudaden haraji da gwamnatin ke karba daga masu kamfanoni.
Ya ce suna sa ran masu zuba hannun jari da dama za su shigo domin bangarorin tattalin arziki da dama domin rage wa gwamnati nauyi, sannan ya yi kira ga gwamnati ta yi dokoki na musamman da za su kula da harkokin inganta tattalin arzikin kasa.
Farfesa Adeola Adenikinju na Tsangayar Tsimi da Tanadi na Jami’ar Ibadan cewa ya yi akwai bukatar gwamnati ta magance asarar da take tafkawa a bangaren man fetur ta hanyar yaki da masu fasa bututun man da sauransu, sannan ta gyara matatun man da ke kasar nan.
Ya ce dole gwamnati ta tabbatar da tsaro ya inganta idan har tana so a samu ci gaba mai dorewa.
Tinubu ya raina ’yan Nijeriya — LP da PDP
A martanin Jam’iyyar LP kan jawabin Shugaban Kasa na Sabuwar Shekara, jam’iyyar ta ce jawabin ya nuna cewa Shugaban ba ya da tausayi.
Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar, Obiorah Ifoh ne ya bayyana haka, inda ya ce, “Akwai takaici yadda Shugaban Kasar da hadimansa ba su yi tunanin bayyana sama da mutum 200 da ’yan ta’adda suka kashe a daren Kirsimeti a Jihar Filato ba.
Wannan ai abin kunya ne. Shugaban ya nuna gazawa wajen inganta ababen more rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki da karyewar darajar Naira da sauransu, saboda yadda ya kasa yin gamsasshen bayanin wadannan abubuwa a jawabinsa.”
A bangaren Jam’iyyar PDP cewa ta yi jawabin na Shugaban Kasa zantukan ne na yaudara, kamar yadda Sakataren Watsa Labaran Jam’iyyar, Debo Ologunagaba ya bayyana.
Ya ce, “Mutanen Nijeriya na bukatar Shugaban Kasa ya bayyana musu kudaden da aka samu daga janye tallafin man fetur.”
Sannan ya bukaci Majalisar Dokoki ta Kasa ta jagoranci binciken a matsayinta na, “Mai tabbatar da dimokuradiyya.”
PDP ta caccaki Shugaban Kasar bisa gaza yin bayani game da kashe mutane a Jihar Filato a jawabin, inda ta yi zargin cewa an kashe sama da mutum 5,000 a Nijeriya tun bayan darewarsa karagar mulki a ranar 29 ga Mayun bara.
Mu dai mu gani a kasa kawai — ’Yan Nijeriya
Wani dan kasuwa a Kano ma suna Suleiman Abdullahi ya ce mutane sun fi bukatar Gwamnatin Tarayya ta yi yaki da hauhawar farashin kayayyaki domin shi ne ke cinye musu jari.
“Rayuwa ta yi matukar tsada da wahala saboda yanzu kasuwa ba ta da tabbas. Kusan kullum farashin kayayyaki tashe yake yi, idan ka sayi kaya yau, ba ka da tabbas za ka same shi a haka gobe.
“Wannan matsalar tana matukar karya mana jari,” inji shi.
Muhammadu Hussaini, wanda manomi ne a Jihar Katsina ya ce matsalar tsaro ce babbar matsalarsu, inda ya yi kira ga gwamnati ta yi wani abu, domin su gani a kasa.
“Kasafin kudin ba zai yi wani tasiri ba idan ba a samu tsaro ingantacce ba.
“Ya kamata a muhimmantar da tsaro, lallai akwai bukatar Gwamnatin Tarayya da sauran gwamnatoci a matakai daban-daban da shugabannin addini da sarakuna su yi kara kaimi a wannan bangare.
“Sai da tsaro za a yi komai. “Na ji Shugaban Kasa yana cewa wai za su tallafa wa mutane su noma hekta 500,000. Wannan mai sauki ne, amma idan an samar da tsaro,” in ji shi.
Shi kuma wani matashi mai suna Aiye Adebayo Cyril mazaunin Oke Aro cewa ya yi in dai maganar kasafin kudi ce, to, lallai an dade ana ruwa kasa na shanyewa, inda ya ce idan gaske gwamnati take yi, to ta karfafa dabbaka kasafin tallafa wa marasa karfi da kananan ’yan kasuwa da samar da ayyukan yi ga matasa.
Ita ma Misis Omotoshola Sarimakin da ke zaune a Jihar Legas cewa ta yi ita dai bukatarta ita ce ta gani a kasa kawai, ba kawai a yi ta dogon Turanci ba tare da ganin sakamako ba.
“Ya kamata a rage tafiye-tafiye kasashen waje, a fara ganin muhimman ayyukan a kasa,” in ji ta.