Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kudin da ya kai Naira biliyan 350 na shekarar 2024 a gaban Majalisar Dokokin Jihar a ranar Juma’a.
A cikin kasafin dai, fannin ilimi ne ya sami kaso mafi tsoka na Naira biliyan 95.
Gwamnan dai ya yi wa kasafin na badi lakabi da “Kasafin farfadowa da kuma sauyawa”, inda ya ce sun tsara shi ne domin ya yi daidai alkawuran da suka yi al’ummar Jihar a yayin yakin neman zabensu.
A cikin kasafin dai, Abba ya ce al’amuran yau da kullum za su lakume Naira biliyan 134.4, yayin da albashin ma’aikatan gwamnati da na masu rike da mukaman siyasa da alawus-alawus dinsu zai lashe Naira biliyan 85.74, sai al’amuran gudanarwar gwamnati da za su sami Naira biliyan 78.4.
Kazalika, Gwamnan ya ce manyan ayyuka za su lashe Naira biliyan 215, kwatankwacin kaso 62 cikin 100 na kasafin.
Ya kuma ce an ware wa bangaren ilimi Naira biliyan 95.4, sai lafiya mai biliyan 51.4, sai ayyuka da gidaje mai biliyan 40.4, sufuri mai biliyan 4.8, yayin da tsara birane biliyan 5.1, shi kuma aikin gona aka ware masa Naira biliyan 11.
Abba ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba bunkasa rayuwar al’umma muhimmanci a mulkinta, amma ya za su tabbatar sun toshe duk wata kafar zirarewar dukiyar gwamnati.
Ya ma ce gwamnatin za ta kafa wani kwamiti na dindindin da zai tabbatar da ana bin gaskiya sannan ana yin komai bisa bin doka a dukkan hukumomi da ma’aikatun gwamnatin Jihar.
Da yake mayar da jawabi, Kakakin majalisar, Jibril Isma’il Falgore, ya yi alkawarin cewa majalisar za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta kammala aiki a kan kasafin a kan lokaci kuma ba tare da ta tsallake duk matakan da doka ta tanada ba.