Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattijai, Sanata Shehu Sani, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kaduna, tare da rushe duk tabargazar da ya ce Gwamna Nasir El-Rufa’in ya yi a Jihar.
Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawarsa da gidan rediyon Invicta FM da ke Kaduna.
- Gwamnan Ribas ya haramta karuwanci da ‘night club’ a Fatakwal
- Babban basaraken Jihar Oyo, Olubadan na Ibadan, ya rasu
A wani shaguben da ake ganin da El-Rufa’in yake, Shehu Sani ya ce duk mutumin da yake zagi ko cin mutuncin mutane bai cancanci shugabanci ba, ko a addinance.
Ya ce ya rage wa jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar ta hada kan mambobinta wajen ganin ta samu nasara a zaben na 2023.
“Mun zauna da magoya bayana, kuma suna so na tsaya takarar Gwamnan Kaduna, kuma zan yi haka don in kawar da APC da dan takarar da Gwamna zai tsayar, da yardar Allah.
“Kwamared zai shiga Gidan Gwamnatin Kaduna, kuma za a rantsar da shi don ya kawo canji, wanda zai kawar da tabargazar da suka yi a Jihar da sunan kawo ci gaba.
“Ina rokon addu’a daga malaman addini da ’yan kasuwa da masu bukata ta musamman da mata da matasa.
“Kun zabi Malam a matsayin Gwamna, yanzu kawai abin da ya rage shi ne ku zabi Kwamared domin ku ga bambanci a tsakaninmu,” inji Shehu Sani.
Sai dai ya ce ba shi da kudin da zai raba wa wakilan jam’iyya yayin zaben fid da gwani, inda ya yi gargadin cewa siyasar kudi ce ta jefa Najeriya a halin da ta tsinci kanta yanzu.
Ya ce muddin talakawa suka zabe shi, ko ba shi da kudi zai yi nasara.