✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Zan nemi shawarar tsayawa takarar shugaban kasa — Kauran Bauchi

Na cika duk wasu muradai na a siyasance.

Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi, ya nemi a bashi makonni uku ya nemi shawarwari dangane da bukatar tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaben 2023.

Gwamnan mai inkiyar Kauran Bauchi ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da wata kungiyar Matasan Arewa ta Northern Youth Leaders Forum (NYLF) ta gabatar masa da wasikar neman ya bayyana bukatar tsayawa takarar a babban zaben da ke tafe.

Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa, Shugabannin Kungiyar bisa jagorancin Elliot Afiyo, sun gana da Gwamnan ne a Dakin Taro na Banquet Hall da ke Fadar Gwamnatin Jihar a Bauchi.

A cewar gwamnan, “a halin yanzu bani amsar da zan baku, amma zan tuntubi sauran abokan huldar siyasa sannan daga bisani na fayyace muku shawarar da na yanke.

“A yanzu na dogora ne da hukuncin Allah da kuma mazaba ta, amma ku bani mako biyu zuwa uku sai ku ji hakikanin abin da na yanke.

“Na cika duk wasu muradai na a siyasance, kuma ni mutum ne da ya taso tun daga matakin karamin ma’aikacin gwamnati har na kawo wannan mataki da nake kai a yanzu.

“Allah Ya albarkaci rayuwa ta da iyalina, saboda haka babu wani abu da nake fafutikar nemansa a rayuwa yanzu domin Allah ya gama cika min burika na.

“Yanzu ba zan iya tabbatar muku da cewa zan tsaya takarar Shugaban Kasa ba, amma zan nemi shawarar masu ruwa da tsaki a kan lamarin.

“Babu wani dan siyasa a fadin Najeriya da ake farautarsa kuma ake son tozarta shi kamar ni.

“Tun a shekarar 2007 da na kayar da wani gwamna mai barin gado na zama Sanata mai wakiltar shiyyar Bauchi ta Kudu har zuwa lokacin da aka nada ni Ministan Abuja, na ci gaba da fuskantar adawa mai tsananin gaske daga bangarorin siyasa daban-daban.

“Sai dai duk da wannan, ban bari hakan ya yi tasiri kan abin da na sa a gaba ba kuma ban sauka daga turbar da nake da yakini a kanta ba.

“Cikin Kaddarawar Allah a yanzu ni aka zaba a matsayin gwamnan Jihar Bauchi duk da waccan adawar da aka rika min da neman a karya lagon siyasata.

“Tabbas Allah Ya min baiwa ba kadan ba,” inji Gwamnan.