Babban Sufetan ’Yan Sanda da Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro sun ja kunnen masu shirin ta da zaune tsaye a babban zabe mai zuwa.
Shugabannin sun yi gargadin ne a wani taron masu ruwa da tsaki ta fuskar tsaro da aka gudanar a Hedikwatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a Abuja a ranar Juma’a
- Matsalar Tsaro: Dalilin da muke neman hadin kan kasashe —CDI
- ’Yan siyasa ku koyi daukar kaddarar faduwar zabe –Babban Limamin Owerri
Mai ba gwamna shawara kan harkar tsaron kasa, Babagana Monguno ya ce, Shugaba Buhari ya ba su cikakken iko su yi maganin duk wani mai son kawo cikas ga zaman lafiya da kuma gudanar da zaben cikin nasara.
Shi kuwa shugaban ’yan sanda, Usman Alkali Baba, cewa ya yi, rundunarsa ta kuduri aniyar ganin cewa an yi zaben na 2023 lafiya.
Don haka ya yi kira ga ’yan siyasa da su kiyaye, da kuma bin doka da oda, su kuma bari jami’an tsaro su yi aikinsu na samar da kariya.
Ya koka kan rahotannin da rundunarsa ke samu na tashe-tashen hankula tun da aka soma yakin neman zabe a wasu wurare; inda jami’ansa suka yi kamen wasu da ake zargi.
A jawabinsa da farko, Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya ce hukumar kawo yanzu, ta samu rahoton fadace-fadace da ya kai 50 a wuraren yakin neman zabe a wasu jihohi a 21 na kasar nan.
Sai ya yi kira da dauki matakan dakile faruwan haka, domin yakin neman zabe cikin lumana, shi zai sa a yi zaben cikin kwanciyar hankali.