Hadaddiyar kungiyar magoya bayan Dogarin tsohon Shugaban Kasa Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha, ta yi barazanar maka shi a kotu matukar ya ki amsa kiranta na fitowa takarar Shugaban Kasa a 2023.
Kungiyar, ta bayyana hakan ne yayin wani gangamin goyon baya da ta shirya na shiyyar Arewa maso Yamma a Kano ranar Asabar.
- Matsalar Tsaro: Birtaniya ta horas da dakaru 145 a Najeriya
- 2023: Dungun da Buhari ya yi ya jefa Osinbajo da Tinubu da sauransu a duhu
A cewar Daraktan tafiyar a shiyyar, Salisu Mu’azu Rijiyar Zaki, muddin gwanin nasu ya ki fitowa takara, tamkar yana kokarin hana Najeriya cin amfanin gogewar da yake da ita ne.
Ya ce, “Mun shirya wannan gangami ne domin mu yi kira ga wannan bawan Allah, Dokta Hamza Al-Mustapha ya fito takarar Shugaban Kasa a 2023.
“A zahirin gaskiya bai ma san muna wannan taron ba a yau, domin wannan kungiya ta masoya ce masu neman ci gaban Najeriya.
“Idan har bai amsa kiranmu ba, a yadda muka kalli gudunmawarsa, wannan kungiya da sauran kungiyoyin sa-kai mun gama yanke hukuncin kai shi kara.
“Abin da ya sa muke goyon bayan Hamza Almustapha shi ne nagartarsa, da kuma yadda ya bayar da gudunmawa wajen ayyukan ci gaban kasa zamanin mulkin Abacha, domin hatta Asusun Man Fetur na Kasa (PTF) shawararsa ce ta sa aka kafa shi, ga kuma raba shiyyoyin siyasa shida, da ma sauran dalilai da dama,” inji Salisu Rijiyar Zaki.
Daraktan ya kuma ce la’akari da gogewar shi a fannin tsaro a matsayin tsohon soja, Almustapha zai taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi Najeriya a halin yanzu.
Sai dai ya ce ya zuwa yanzu ba su yanke jam’iyyar da dan takarar zai tsaya ba, suna dai kokarin ganin ya amsa kiran nasu ne tukunna.
Ita ma da take tsokaci, wata mai goyon bayan tafiyar, Hajiya Kalima Kabir, ta ce a dukkan ’yan takarar, babu wanda zai iya cire wa Najeriya kitse a wuta, musamman a harkar tsaro, face Hamza Almustapha.