✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Za mu hana baki yin zabe a Najeriya —Imigireshan 

Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta kuduri aniyar hana wadanda ba ’yan Najeriya ba kada kuri'a a zaben 2023.

Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta kuduri aniyar hana wadanda ba ’yan Najeriya ba kada kuri’a a zaben 2023.

Ta kuma yi alkawarin tabbatar da ganin an yi zabuka cikin ’yanci, gaskiya, sahihanci tare da hana ’yan baki duk wani nau’i na zaben.

Mataimakin Kwanturola-Janar mai kula da shiyyar ‘C’, ACG Isma’ila Abba Aliyu, ya sanar a Damaturu, Jihar Yobe, cewa Hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hana wadanda ba ’yan Najeriya ba.

“Ko a lokacin yakin neman zabe, yaranmu za su sa ido sosai domin tabbatar da baki ba su shigo ba don shiga cikin harkokin siyasa, saboda wannan yana daya daga cikin lokuta masu mahimmanci.

“Za mu kuma yi amfani da na’urorinmu na zamani don sa ido kan motsin mutane da ake shakku a kansu, dole ne mu yi bayanin kowa don kauce wa yin barna da sunan Najeriya.”

Ya ci gaba da cewa, ba za a ba wadanda ba  ’yan Najeriya damar rike duk wata takarda da aka tanadar wa ’yan Najeriya ba.

“A kwanakin baya CG dinmu a Abuja ya shaida mana cewa an kwace katuna da yawa daga hannun wadanda ba ’yan Najeriya ba saboda ba su da dalilin rike katin Najeriya.

“Wadannan takardu an yi su ne ga ’yan kasa kawai, kuma hakan  babbar barazana ce ga tsaron Najeriya; Yaranmu za su ci gaba da kame”.