✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Yadda baraka ke karuwa tsakanin Buhari da Tinubu

Rabon Buhari da Tinubu su hadu tun ranar 7 ga Janairun 2020

Barakar da ta bulla a tsakanin magoya bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da na Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ta fadada.

A yayin da zaben 2023 ke karatowa, amma rabon Buhari da Tinubu su hadu tun ranar 7 ga Janairun 2020, lokacin tsohon Gwamnan Jihar Legas din ya ziyarci Fadar Shugaban Kasa a Abuja; Majiyoyi kuma sun yarda cewa akwai tsama a tsakaninsu.

Wani malamin jami’a kuma masanni kan kulle-kullen siyasa a Najeriya ya ce da gangan aka kirkiro barakar domin mayar da Tinubu saniyar ware da zimmar share hanyar da wani dan takarar na daban zai samu tikitin jam’iyyar na takarar shugabancin kasar a 2023.

Aminiya ba za ta iya hasashen lokaci na karshe da mutanen biyu suka yi magana ta waya ba; amma majiyoyi da yawa sun ce akwai tsamin dangantaka a tsakaninsu.

Bayan ya yi kokarin samun shugabancin kasa har sau uku, Buhari ya yi kawance da Tinubu da wasu mutane domin kafa Jam’iyyar APC a 2013, kawancen da ya kai shi ga nasararsa a 2015.

Jim kadan da hawan Buhari mulki, ba a ga Tinubu a kusa da Fadar Shugaban Kasa ba har sai a shekarar 2018 lokacin da batun zaben 2019 ya taso.

 

Dangantakarsu tana nan daram —Garba Shehu

Sai dai kuma kakakin Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya ce babu wata baraka tsakanin Buhari da babban amininsa, Tinubu.

Garba Shehu, a cikin wata sanarwa, ya ce Shugaban Kasar da Asiwaju suna da cikakkiyar sadaukarwa ga APC don kawo canji.

“Wannan sadaukarwa ce da suke da ita ga al’ummar Najeriya. Rahotannin baya-bayan nan da ke cewa akwai tsama a tsakanin shugabannin biyu na jam’iyyarmu ba gaskiya ba ne; aikin wadansu masu muguwar manufa ce.

“Abin takaici ne wasu kafafen labarai su rika haifar da cece-ku-ce suna kafa hujja da labarin kanzon kurege da wadansu ke kirkirowa wadanda ba gaskiya ba ne.

“Wannan gwamnati tana sane da masu kitsawa da yada labarai marasa tushe domin sanya shakku a zukatan jama’a game da alakar da ke tsakanin shugabannin biyu da kuma ko jam’iyyar za ta kasance a dunkule ko a’a,” inji shi.

Kakakin Shugaban Kasar ya kuma ce, “A wajen Shugaba Buhari, Tinubu zai ci gaba da kasancewa daya daga cikin shugabannin siyasar da aka fi girmamawa a kasar nan, wanda ya tsayu kan akidunsa ya fuskanci dukkan kalubale.”

 

Kwanton da Tinubu ya yi

Tun lokacin da Shugaba Buhari ya fara zango na biyu, tsohon Gwamnan Legas din ya ziyarce shi ne kawai a wasu ’yan lokuta kuma duk da bullar cutar coroanvirus, Shugaban ya rika karbar bakuncin manyan ’ya’yan jam’iyyar.

Duk da cewa Tinubu ya dauki lokaci ba ya kasar, ana fassara “nisantar Fadar Shugaban Kasa” da ya yi a matsayin wata alama da ke nuna rashin jituwa a tsakanin bangarensa da na Shugaba Buhari.

A ziyararsa ta karshe a ranar 7 ga Janairun 2020, Tinubu ya bayyana Shugaba Buhari a matsayin mutum mai hali nagari da jajircewa wanda ba zai taba yarda da tayin wa’adin shugabanci karo na uku ba.

Gabanin haka, sun taba yin ganawar sirri a ranar 2 ga Nuwamban 2018.

Kafin waccan ganawar, a ranar 31 ga Oktoban 2018, Tinubu ya gana da Buhari kuma ya yi watsi da kiran da ake yi cewa Shugaban Jam’iyyar ta Kasa na lokacin, Kwamared Adams Oshiomhole ya yi murabus.

Amma da yake bayani kan rashin ganin Tinubu a Fadar Shugaban Kasa har na tsawon lokaci, Malam Garba Shehu ya ce Tinubu ba Minista ba ne da za a rika ganinsa koyaushe.

Ya ce, kuma in ba a cika ganinsa ba, hakan ba zai sa a ce shi ba abokin Shugaban Kasa ba ne, ko ba ruwansa da gwamnatin.

 

Yadda gwamnoni suka raunana tasirin Tinubu

Duk da kokarin da Tinubu ya yi na ganin ya ceto Oshiomhole, wani jigo a bangarensa, sai da Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) na Jam’iyyar APC ya tsige shi.

Cire Oshiomhole tare da sahalewar Buhari, ya raunana tsagin Tinubu kuma ya bai wa gwamnoni damar yin kane-kane a harkar gudanar da jam’iyyar.

Bayan cire Oshiomhole ne Gwamna Mai Mala Buni ya zama Shugaban Kwamitin Rikon Jam’iyyar ta Kasa.

Sau biyu ana kara wa’adin kwamitin kuma wasu rahotanni na cewa ana iya dage Babban Taron Jam’iyyar na Kasa da aka shirya gudanarwa a watan Yunin 2021, domin share wa kwamitin rikon fagen ci gaba da tafiyar da lamura.

Masu ruwa-da-tsaki na jam’iyyar na nuna shakku kan kirarin da Gwamnan Jihar Jigawa kuma Shugaban Kwamitin Tuntuba na Jam’iyyar, Muhammad Badaru Abubakar, ya yi cewa ba za a dage ranar gudanar da taron ba.

Aminiya ta ruwaito cewa gwamnoni ne suke juya akalar jam’iyyar, musamman uku daga cikinsu wato Buni da Badaru da Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, tare da goyon bayan Fadar Shugaban Kasa.

A watan Oktoban 2020 yayin zanga-zangar #EndSARS, Tinubu ya kasance cikin wadanda aka fi nuna wa yatsa bayan da aka zarge shi da kasancewa daya daga cikin wadanda suka dauki nauyin zanga-zangar.

Sai dai magoya bayan jagoran na jam’iyyar APC sun bayyana zargin a matsayin shifcin gizo, suna cewa yana daga cikin wadanda suka yi asara mai yawa, don haka ba zai yiwu ya zama mai daukar nauyin tarzomar ba.

Da yake magana a yayin wani shirin gidan Talabijin din Channels, Tinubu ya ce wadansu mutane sun yi wa Fadar Shugaban Kasa karya cewa shi ne ya shirya zanga-zangar.

 

‘Ana matsa wa Buhari ya yi watsi da Tinubu’

Wani daga cikin iyalan Shugaban Kasar ya ce akwai yunkurin shawo kan Buhari domin ya goyi bayan dan takarar da zai kare muradinsa idan ya sauka daga shugabancin kasar a shekarar 2023.

“Mun yi imanin cewa Tinubu ba zai kare muradun Buhari ba bayan mulkinsa, saboda haka akwai bukatar neman wani na daban.

“Muna aiki tukuru domin shawo kan Shugaban ya dafa wa dan takarar da zai kare muradunsa bayan mulkinsa,” inji majiyar, wacce ta nemi a sakaya sunanta.

Hakazalika, wani mamba a Majalisar Ministocinsa ya ce: “Shugaban Kasar ba ya sha’awar takarar Tinubu saboda bai gamsu cewa Asiwaju ne mutumin da ya dace ya gaje shi ba.”

Sai dai Aminiya ta ruwaito cewa Tinubu bai fito fili ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Shugaban Kasa ba, amma kungiyoyi daban-daban suna yi masa kamfen a bayyane.

 

Ambode da Omisore da wasu su ‘dankwafar’ da Tinubu

A abin da wasu ke gani daya ne daga cikin matakan rage tasirin Tinubu a Kudu maso Yamma, Jam’iyyar APC mai mulki na ci gaba da kawo mutanen da ake ganin suna adawa da tsohon Gwamnan na Jihar Legas.

Tsohon Gwamnan Jihar Legas, Akinwunmi Ambode, wanda yunkurinsa na sake tsayawa takara a karo na biyu a 2019 bai yi nasara ba saboda Tinubu ya yake shi, a ranar Talata aka bayyana shi a matsayin mamba a Kwamitin Tuntuba na Jam’iyyar.

Baya ga Ambode, jam’iyyar ta fito da jiga-jigan jam’iyyar a shiyyar Kudu maso Yamma, ciki har da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Osun, Iyiola Omisore da tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Gbenga Daniel, da tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Dimeji Bankole da sauransu.

Akwai rahotannin da ke cewa Jam’iyyar APC ta jawo su ne don su kawar da Tinubu gabanin shekarar 2023.

Abin da ya sa barakar za ta dore —Jiga-jigan APC

Da take magana game da alakar Buhari da Tinubu, wata majiya daga Fadar Shugaban Kasa ta ce, “Buhari bai taba dasawa da Asiwaju ba. Kawai ya yi imanin cewa ya kamata ya yi amfani da tsohon Gwamnan na Legas ne domin cimma burinsa. Bayan zaben 2015, za ku tuna cewa an yi watsi da Asiwaju.

“An sake kawo shi kusa kafin zaben 2019. Don haka, babu bukatar damuwa game da alakarsu,” inji shi.

Wani babban dan Majalisar Tarayya a APC ya shaida wa Aminiya cewa Shugaban bai ji dadin abubuwan da ke faruwa a Kudu maso Yamma ba kuma yana zargin Tinubu da kasa yin wani abu a bayyane domin kashe wutar da ta tashi a yankin.

“Zan iya tabbatar muku cewa Shugaban Kasa ba zai fito fili ya mara masa baya (Tinubu) ya zama Shugaban Kasa ba, duk da cewa tsohon Gwamnan na Legas ya yi imanin cewa wannan ne lokacin da ya kamata a saka masa, idan aka yi la’akari da dimbin aikin da ya yi wa Buhari da APC.

“Har ila yau, Shugaban Kasar yana da jikakka da Tinubu saboda yana masa irin kallon da yake yi wa kowane dan siyasa a kasar nan. Amma ya fara dari-dari da shi (Tinubu) a lokacin da ya fara ikirarin shi ne Jagoran Jam’iyyar APC ta Kasa bayan zaben 2015.

“Kamar yadda kuka sani, mai mulkin kasa ne ya kamata ya zama jagoran jam’iyya. Ka sani, tsohon gwamnan na Legas yana da girman kai, shi kuma Shugaban yana da taurin kai, su biyun ba za su iya tafiya tare ba,” inji shi.

 

‘Baraka tsakanin Buhari da Asiwaju jita-jita ce kawai’

Amma wani jigo a jam’iyyar kuma na kusa da Shugaba Buhari da Tinubu, ya ce babu wata baraka a tsakanin mutanen biyu.

A wata hira ta wayar tarho, ya ce: “Kun san lokacin da zabe ke gabatowa mutane za su so su rura wutar rikici kuma kowane irin sokiburutsu zai kasance a kafofin watsa labarai.

“A wurina, wannan abu ne na al’ada a yanayin siyasar kasar nan. Ko da Buhari, ko babu shi, tasirin Tinubu a Kudu maso Yamma ba za a iya kawar da shi ba.”

 

Magoya bayan Tinubu na neman mafita

A yankin Kudu maso Yamma, musamman Legas, inda batun takarar Tinubu ya yi kamari, magoya bayansa suna sa ido sosai kan abubuwan da suke faruwa da kuma binciko wasu hanyoyi gabanin zabe.

Da yawa daga cikinsu sun yi amanna matakin Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) na bude sabon bincike a kansa, ya samo asali ne daga sabanin da ke tsakaninsa da Shugaban Kasar.

Kuma magoya bayan Tinubun sun ce abin bai yi musu dadi ba, inda suka bayyana binciken da cewa ‘yaki ne aka kaddamar a kansa.

Kakakin Jam’iyyar APC a Jihar Legas, Seye Oladejo ya ce hare-haren da ake daukar nauyin kai wa Tinubu ba za su iya dakatar da shi ba.

Ya ce, “Rikicin ya ci gaba a fagen jita-jita mara amfani. Duk da haka, tarihin wannan lokaci ba zai cika ba tare da rawar da Tinubu ya taka wajen rusa Jam’iyyar PDP ba ta hanyar adawa.

“Ya kamata ’yan kanzagin Fadar Shugaban Kasa su ci gaba da rayuwa cikin yaudarar kai har zuwa lokacin da aka tsara,” inji shi.

 

Ana amfani da Fadar Shugaban Kasa don rage kaifin Tinubu —Farfesa

Da yake bayyana yadda lamarin yake, wani masanin siyasa a Jami’ar Abuja, Abubakar Umar Kari, ya ce ana amfani da Fadar Shugaban Kasa ne domin rage kaifin Tinubu.

A wata hira da aka yi da shi, Farfesa Kari ya ce: “Ba za a samu wata fitina ta hakika a tsakanin shugabannin biyu ba kan batun dangantaka ta mutum da mutum ko bambancin siyasa.

“Ba ni da masaniya game da wani lamari, ko wata matsala ko rashin jituwa ko kuma wani sabani da ke nuna rabuwar kawuna a tsakanin su biyun.

“A dabi’ance, Buhari ba ya da sakin jiki sosai, ba ya mu’amala a sarari, kuma ba ya nuna zumunci. Wannan shi ne dalilin da ya sa wadansu mutane ke zargin sa da rashin kula da lamarin wadansu.

“Saboda wannan dalili, wadansu mutane suna ganin Buhari na da son kai kuma ba ya damuwa da kowa, musamman yanzu da ba ya neman komai daga kowa. Ina daya daga cikin wadanda ke ganin Buhari ba zai taka wata muhimmiyar rawa a siyasar 2023 ba,” inji shi.

A cewar Farfesa Kari, akwai wadansu mutane masu karfi, na kusa da Shugaban Kasar wadanda ke amfani da sunansa don su cimma burinsu na siyasa.

“Yawancinsu suna adawa da Tinubu da kuma burinsa na shugabancin kasar nan. Su ne ke kirkira da yada ra’ayin cewa ba komai a tsakanin Tinubu da Shugaban Kasa,” inji shi.