Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’Ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar shugabancin kasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa.
A cewarsa, goya wa Tinubu baya ra’ayi ne na kashin kansa da kuma gamsuwa da ya yi da lamarin dan takarar, yana mai cewa bai hana mabiyansa kowa ya zabi nasa ra’ayin ba.
- NAJERIYA A YAU: Shin Kuri’un ’Yan Najeriya Za Su Yi Tasiri a Zaben 2023?
- Gobara ta lalata kayan N23bn a wata 3 —Hukumar Kashe Gobara
“Kwamitin zartarwa na JIBWIS ya yi zama inda ya bukaci mambobinsa kowa ya bayyana ra’ayinsa dangane da dan ktakarar Shugaban Kasar da yake ra’ayi.
“Yayin zaben, Atiku ya samu kuri’u 73, Tinubu 13, sauran kuma sun ce inda nake su ma nan suke.
“Tinubu zan zaba, wannan shi ne ra’ayina, ku ma kuna da damar zaben wanda kuka yi ra’ayi,” in ji malamin.
Sheikh Jingir ya bayyana haka ne ranar Lahadi sa’ilin da yake jawabi a wajen rufe taron kara wa juna sani na kasa na JIBWIS karo na 30 da ya gudana a Jos, babban birnin Jihar Filato.
Malamin ya yi kira ga Tinubu da ya zama mai adalci ga kowa ba tare da nuna bambanci na addini ko kabila ba, idan Allah Ya ba ba shi nasarar lashe zabe mai zuwa.
Kungiyar ta ba da tabbacin za ta ci gaba da yada harkokinta daidai da karantarwar Al-Kur’ani da Sunnah domin samar da cigaba mai ma’ana a dukkanin fannonin rayuwa.