Da ba don sabata-juyata irin na siyasa ba da Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ne ya zama dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP a 2019.
Sa’o’i kadan kafin babban taron 2018 a Fatakwal, a bayyane take cewa Tambuwal wanda shi ne Shugaban Majalisar Wakilai na 10, da ke samun goyon bayan Gwamnan da ya karbi bakoncin taron, Nyesome Wike, ya kamo hanyar kalubalantar Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.
Ya kasance daya daga cikin mutum 12 ciki har da uku daga Arewa maso Yamma da suka yi zawarcin tsaya wa Jam’iyyar PDP takarar Shugaban Kasa a zaben fitar da gwani da ya gudana a Fatakwal, ranar 6 ga Oktoban 2018.
Lura da lissafi irin na siyasa, a lokacin, an fi tsammanin Tambuwal ya samu nasara bisa la’akari da yadda ya bijiro da takarar tasa. Batutuwa da dama ciki har da karancin shekarunsa – idan aka kwatanta da abokan takararsa – da gogewarsa a siyasa da rashin zargin cin-hanci a kansa – sun taimaka gaya wajen yiwuwar samun nasararsa a zaben fitar da gwanin.
Kwatsam sai sama ta koma masa kasa a karshen zaben dan takarar, inda ya zo na biyu da kuri’a 693 ya rufa wa Atiku baya wanda ya yi nasara da kuri’a 1,532.
Bukola Saraki ya samu kuri’a 317 sai Sanata Kwankwaso mai kuri’a 158. Ba tare da bata lokaci ba, Tambuwal ya koma jiharsa Sakkwato inda ya yi takarar Gwamna a wa’adi na biyu; ya doke tsohon Mataimakinsa kuma dan takarar Jam’iyyar APC, Ahmad Aliyu da kuri’a 342 kacal a zaben Gwamnan.
Yanzu Tambuwal ya sake komowa ruwa yana neman tikitin tsaya wa babbar jam’iyyar hamayya – PDP – takara, sai dai da akwai tarnaki mai yawa a gaban lauyan mai shekara 56 da lallai ya tsallake su idan yana son ya yi nasara a wannan karo.
Yanki da addini:
Batun karba-karbar kujerar Shugaban Kasa ba abu ne da Tambuwal da magoya bayansa za su yi banza da shi ba, musamman da yake gwamnoni da masu ruwa-da- tsaki daga Kudu sun ci gaba da tsayawa kai-da-fata cewa lallai yankin ne zai samar da Shugaban Kasa bayan karewar wa’adin Muhammadu Buhari.
Suna kafa hujja ce da batun wanzar da daidato da adalci.
Kamar Shugaba Buhari da wa’adinsa na shekara takwas zai kare a badi, Tambuwal ma dan yankin Arewa maso Yamma ne.
Lallai ne Gwamnan Jihar Sakkwaton ya gamsar da sauran yankunan cewa yankin Arewa maso Yamma ne zai sake samar da Shugaban Kasa.
Wani abu kuma har wa yau, shi ne batun addini.
Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, (CAN) da kuma takwararta ta Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN), sun bayyana karara cewa mabiyin addinin Kirista ne ya dace a mara wa baya ya zama Shugaban Kasa a badi.
Shugaban Kungiyar PFN, Bishop Francis Wale Oke, kwanan baya an ruwaito shi yana cewa: “Ba ma son Musulmi ya sake shugabancin kasar nan a 2023. Ba ma son hakan sam. Ba daidai ba ne. Musulmi ya shugabanci kasar nan tsawon shekara takwas, majami’u sun mara masa baya. Mun yi addu’o’i kuma ba ma nadamar haka.”
Sai dai Kungiyar Kare Hakkokin Musulmi ta Najeriya, (MURIC), ta ce dole ne Musulmi ya ci gaba da mulkin Najeriya a badi. Sai dai, ta karkata ga Musulmin ya zama dan Kudu.
Ta ma zayyana sunayen wadansu Yarbawa Musulmi su takwas da ta yi ikirarin suna da “matukar nagarta” wajen shugabancin kasar nan.
Tambuwal Musulmi ne daga Arewa Sai dai tsohon Shugaban Majalisar Wakilan, ya yi watsi da matakin da gwamnonin Kudu suka dauka cewa ba zai biyayya ga matakin ba.
“Kai, na fa bayyana matsayata karara game da batun nan – cewa a lokacin da gwamnonin Kudu suka zauna suka fito da wannan matsaya tasu, takwarorinsu na Arewa ma sun yi taro a Kaduna inda suka bayyana matsayarsu. Ni kuma Gwamna ne daga Arewa, don haka ba ruwana da matsayar da gwamnonin Kudu suka dauka a kungiayarsu,” kamar yadda aka ruwaito shi yana fada yayin wata tattaunawa a kwanakin baya.
Wakilai masu zabe daga Kudu:
Manyan wadanda suka mara wa takarar Tambuwal a 2018 su ne gwamnonin Kudu, musamman Gwamna Wike na Jihar Ribas da tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose.
Sai dai gwamnonin Kudun sun shelanta cewa lallai ne Shugaban Kasa na gaba ya fito daga yankin.
Wike, ya kasance mai daga murya kan batun tare da nanata cewa yana da ra’ayi iri guda da na Gwamnonin Kudu.
Gwamnonin ne ke iko da wakilan jam’iyya masu zabe. Za a iya cewa yana da matukar wahala Tambuwal ya samu tikitin Jam’iyyar PDP ba tare da samun goyon bayan wakilan jam’iyyar daga Kudu ba.
Zakulo Mataimakin Shugaban Kasa:
Neman mara bayan gwamnonin Kudun zai zama wani sabon tarnaki ga Tambuwal, a wajen zabar wanda zai rufa masa baya a matsayin Mataimakin Shugaban Kasa, idan har ya yi nasara ma ke nan a zaben fitar-da-gwani na jam’iyyarsa.
Cikin gaggawa, Atiku, ya iya zille wa gwamnonin a batun zabar Mataimaki a 2018 inda ya bayyana Peter Obi a matsayin Mataimakinsa kafin gwamnonin su ankara. Hakan ya zo wa Atiku cikin sauki ne saboda sai a gargarar karshe ya iya samun gwamnonin suka mara masa baya; bayan wadansu ‘Janar-Janar’ sun sa baki.
Amma idan Tambuwal din zai iya shawo kan gwamnonin jam’iyyarsa daga Kudu wajen sarayar da kudirinsu na samar da Shugaban Kasa; to zai yi zaman shiri da su wajen zabo Mataimakin Shugaban Kasar.
A fili take cewa gwamnonin yankin, wadanda wa’adin mulkinsu na biyu ke karewa a badi; suna lissafin makomar siyasarsu.
Abin tambaya a nan, shin wane ne zai yi wa Tambuwal mataimaki daga cikinsu?
Bakar siyasa da yarfe:
Ba sabon labari ba ne yadda siyasar Najeriya ke cike da bakaken maganganu da yarfen siyasa, sannan akwai fargaba A tsakanin jiga-jigan Jam’iyyar PDP cewa ko Tambuwal zai iya yin salon wannan siyasar?
Kafin zaben fitar da da takarar Shugaban Kasa na jam’iiyar a 2018, an soki Tambuwal game da yadda ya gaza ‘dira’ kan Shugaba Buhari a duk gangamin yakin neman zabensa.
Yayin da sauran ’yan takarar irin su Atiku da Saraki da Kwankwaso aka jiyo amonsu suna sukar lamirin gwamnatin Buharin; Tambuwal ya rika yin taka-tsantsan a kalaman da yake amfani da su.
Daga bayan an ma ce hakan yana daga dalilan da ‘Janar-Janar’ din PDP suka ce Atikun ne dan takarar da ya fi cancanta a 2018.
“Tambuwal mutum ne mai son yin siyasar wayo kuma marar cutarwa. Bai shirya wa yin fitona-fito a siyasa ba. Za ka yi haka ne kawai idan kai dan takarar jam’iyya mai mulki ne amma idan dan takarar hamayya kake, dole ka bukaci wanda zai zakulo lam’o’in gwamnatin da ke kan iko. Kowanenmu ya ga yadda APC ta rika yi wa Jonathan yarfe iri-iri gabanin zaben 2015. An yi masa kazafi iri-iri an kira shi da miyagun sunaye, an zarge shi da abubuwan da ba ya da alhaki a kansu; inda aka tunzara jama’a suka yi masa ca,” inji wani jigon Jam’iyyar PDP.
Jigon na PDP wanda ya bukaci Aminiya ta sakaya sunansa, ya ce PDP tana bukatar dan takarar Shugaban Kasa wanda a shirye yake ya caccaki matsalolin da ke tattare da gwamnatin APC.
“Fiye da shekara bakwai bayan hawa karagar mulkin kasar nan da APC ta yi, har yanzu wa PDP take dora wa alhakin sukurkucewar lamuran kasar nan. Ka dubi abin nan! Don haka, muna bukatar dan takarar da a shirye yake idan suka ce ‘kule’, ya ce musu ‘cas,’ da zai bankado illolinsu ya nuna su ta yadda jama’a za su gan su tsirara,” inji shi.
Sanayyar jama’a a siyasance:
Koda dai Tambuwal ba sabon yankan rake ba ne a siyasance, amma shin zai iya bugun kirjin hada jama’a a siyasance a ciki da wajen Jam’iyyar PDP kamar Alhaji Atiku Abubakar?
A kowace jam’iyyar siyasa akwai masu nada shugabanni, wadanda ba lallai ne suna da kuri’a tasu a yayin babban taron jam’iyya, amma suna da tasiri kan sakamakon zaben.
Galibin masu zawarcin takarar Shugaban Kasa kan ziyarci ireiren wadannan kusoshin jam’iyya domin neman tubarrakinsu.
A Jam’iyyar PDP, tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da tsohon Shugaban Soji Ibrahim Babangida da tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Theophilus Yakubu Danjuma da kuma tsohon Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Aliyu Gusau suna daga cikin wadannan manyan ‘Janar-Janar’ da suke da karfin fada-a-ji.
Masu sharhi sun yi amanna cewa gazawar Tambuwal ta samun cikakken goyon bayansu shi ne silar kasa samun tikitin yi wa jam’iyyar takarar Shugaban Kasa a 2018.
Shi kansa ya tabbatar da hakan yayin wata hira da jaridar Daily Trust da Aminiya suka yi da shi a kwanakin baya.
“Kawai batu ne siyasa da daunin iko da tuntuba da hada jama’a daban-daban. An samu wadansu gungu da manyan mutane da suke jin cewa Atiku Abubakar za su mara wa baya a matsayin wanda ya fi dacewa da takarar jam’iyyar, kuma sun iya gamsar da sauran shugabannin; to ka ji yadda lamarin ya kaya kuma na rungumi sakamakon hannu biyu,” ya fada bayan da aka tambaye shi kan yadda ya kasa samun tikitin yi wa jam’iyyar takara a 2018.
Sannan me za a ce Tambuwal ya yi daga 2018 zuwa yanzu don ya zama dan lelen jiga-jigan masu fada-a-ji na jam’iyyar? Shin ya iya gamsar da su cewa ya fi kowa damar yin nasarar lashe zaben 2023?
Masu sharhi suna da ra’ayin cewa Tambuwal ba ya da nauyin aljihu irin na su Alhaji Atiku a Jam’iyyar PDP ko Asiwaju Bola Tinubu na Jam’iyyar APC in har ya samu tikitin takarar.
Yin takara a matsayin dan hamayya yana da bukatar nauyin aljihu sosai.
Duk da ire-iren gangamin da kungiyoyin fararen hula suke yi, sayen kuri’u har yanzu ya yi kanekane a zabubbukan Najeriya.
Hakan bai rasa nasaba da bakin talauci da jahilcin da suka samu gindin zama a kasar nan wanda hakan ya sa wadansu masu zaben suke sayar da kuri’unsu a kan abin da bai wuce Naira 500 ba.
Matsalar tsaro:
Har yanzu, rashin tsaro ya kasance daga cikin manyan kalubalen da suka yi wa kasar nan dabaibayi. Ta’addanci da ayyukan ’yan fashin daji da sace mutane da rigingimun kabilanci – sun taru sun kara dagula lamarin tsaro a kasar nan.
Yayin da galibin hukumomin tsaro suke karkashin kulawar Gwamnatin Tarayya, masu suka na da ra’ayin cewa Jihar Sakkwato ta fuskanci karuwar hare-hare a ’yan watannin da suka gabata.
Ana cewa Tambuwal ya kasa nuna shugabancin da ya dace wajen taka birki ga wasu hare-haren a jiharsa.
Ga kuma batun da ake yi cewa jihar tana da barayin daji wadanda suke karbar haraji daga al’ummomin jihar.
Tambuwal ya taka muhimmiyar rawa a matsayin Shugaban Majalisar Wakilai amma ana sanya alamomin tambaya ko me ya yi bayan hawansa karagar mulkin Jihar Sakkwato tun daga 2015?