Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda, ya ce zai zama tamkar batanci idan ’yan Najeriya suka ki zaben dan takarar shugabancin kasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, a matsayin kyauta ta musamman daga Allah.
Ya bayyana haka ne a wajen taron kara wa juna sani da kwararru na APC suka shirya kan manufar Tinubu a Cibiyar Taro ta Yar’adua da ke Abuja ranar Laraba.
- Kotun Kano ta daure alkalai kan badakalar kudin marayu N99m
- Kuskuren shekara 24 ne ya jefa Najeriya halin da ta ke ciki — Kwankwaso
Ya ce “Mutum ne mai kishin kasa kuma wannan shi ne wanda muke bukata a yau a matsayin shugaba.
“Babu wanda zai yi tantama kan cigaban da Legas ta samu, kuma muna iya ganin siffofin shugaba nagari a tattare da shi.
“Mun san da cewa dan gwagwarmayar yaki da rashawa ne, kuma kowa ya san da haka. Da a ce akwai rashawa Legas, da ba ta kai inda take ba a yau.
“Zai kasance, ko in ce batance ne juya wa masa baya. Akalla zai tsaya muku, kuma mai kishin kasa ne wanda shi muke bukata a yau a matsayin jagora.
“Duk inda aka samu rashawa cigaba ba zai samu ba, tattalin arziki ba zai bunkasa ba.
“Bai yiwu mu ce babu rashawa a cikin al’umma, amma akalla an kassara ta,” in ji shi.
Yuguda ya kuma ce Tinubu ya fi dacewa ya gaji Buhari saboda nagartarsa da kuma kasancewarsa mai gwagwarmayar yaki da rashawa.
Da take tsokaci a wajen taron, mai dakin Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu, ta ce mijinta zai cire ahali da dama daga kangin talauci da yunwa muddin aka zabe shi Shugaban Kasa a zabe mai zuwa.