Hadimin dan takarar Shugaban Kasar na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, bangaren yada labarai, Phrank Sha’ibu ya ce ko ba kuri’un Gwamnonin G-5 za su iya lashe zaben 2023.
Sha’ibu ya bayyana hakan ne a wata hira da ya gudanar a wani gidan Talabijin mai zaman kansa a Najeriya, inda ya ce batun da jagoran Gwamnonin da ke kiransu G-5 ke yi cewa kofar sulhu tsakaninsu da Atiku ta kusa rufewa, sam bai dame su ba.
- An gurfanar da alkalin bogi kan badakalar N10.6m a Kano
- Hana acaba a Legas ya kawo wa ‘sana’armu’ cikas – Dan fashi
“Tawagar yakin neman zabenmu ta ajiye wannan batu a gefe. Dama kuma mun fada tun a farko cewa mu don Najeriya muke yi ba PDP kadai ba.
“Atiku ba shi da wata matsala ta radin kai tsakaninsa da Wike. Amma sai nake karantawa a jarida cewa Wike ya ce sun kusa rufe kofar sulhu da shi.
“To ko sun rufe kofar ai tagar a bude take, kuma Atiku dan siyasa ne ba mai laifi ba. Kuma ba ta tagar ya shiga siyasar ba, ta kofa ya shiga.
“Sannan Gwamna Wike mutum guda ne, mai kuri’a daya, haka ma sauran Gwamnoni hudu na G-5,” in ji shi.