Shugaban Kungiyar matasan Arewa ta GBC ya bayyana cewa korafe-korafen da Kungiyar Gwamnonin shiyyar Kudu ke yi na karbar mulki ba shi ne mafi alheri ga kasar nan ba.
Kungiyar ta bayyana wannan matsayi nata a wani taron manema labarai da ta gudanar ranar Talata da ta gabata a Abuja.
- Mahaukaciyar guguwa ta hallaka sama da mutum 100 a Amurka
- An gano jaririyar da aka sace daga Neja a Kano
Shugaban Kungiyar Kwamared Bilal Sidi Abubakar ya ce maganar mulki ya koma Kudu daga Arewa sam bai ma taso ba, domin da ma wannan batu yana nan tun 1999 kuma an yi hakan amma ’yan Arewa ba su samu wani ci-gaba ba, “domin haka mu a yanzu muna bukatar nagartaccen shugaba.
Shekarar 2023 wata dama ce ga ’yan Najeriya da za su zabi wanda ya cancanta da zai ciyar da kasar nan gaba,” inji shi.
Ya ce, “akwai tsarin shiyyashiyya tsakanin Arewa da Kudu kuma duk sun samar da shugabanni amma har yanzu mu Arewa muna baya.
“Muna son wanda ya cancanta ya zama Shugaban Kasa a 2023 saboda kasar nan tana fuskantar koma-baya.”
Ya nemi mutanen Arewa da su yi duban tsanaki a cikin ’yan takara, su zabi jajirtaccen da zai kawo shugabanci nagari, wanda kuma zai ciyar da yankin Arewa da ma Najeriya gaba.