Kungiyar magoya bayan Jagoran jam’iyyar APC na Kasa, Bola Tinubu, ya nemi takarar a kujerar shugaban kasa (TSG) na gudanar da taron kaddamar da shugabanninta na jihohi.
Taron da ke gudana a sakatariyar kungiyar ta kasa da ke Abuja ranar Asabar zai baje kolin ayyukan Tinubu tare da rantsar da shugabannin kungiyar na jihohin Najeriya 36.
- Zulum ya haramta bangar siyasa da dabanci
- Mahara sun fasa gidan yari sun saki daruruwan fursunoni a Oyo
Tinubu wanda tsohon gwamnan jihar Legas ne yana da muradin tsayawa takarar shugaban kasa domin maye gurbin Shugaba Buhari a zaben 2023.
Aminiya ta ga dandazon kungiyoyin magoya bayan Tinubu daga sassan Najeriya, daga kowane yanki, sun yi wa wurin taron tsinke.
Taron na zuwa ne mako biyu bayan dawowar jagoran na APC na kasa daga kasar Birtaniya inda ya shafe watanni yana jinya bayan an yi masa aiki.
Dan Majalisar Wakilai, Hon. James Abiodun Faleke, na daga cikin manyan masu jawabi a wurin taron.