Wata Kungiyar Arewa karkashin kungiya mai zaman kanta ta CITAR, ta dage a kan lallai sai Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya tsaya takarar Shugaban Kasa a babban zabe na 2023.
Mai Magana da yawun kungiyar, Hayatu Girie cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a bayan taron da suka gudanar a Jihar Kaduna, ya ce kungiyar ta fara tuntubar dattawa da shugabannin addinai a duk shiyoyin siyasa shida na kasar nan.
- An girke jami’an tsaro 10,000 domin zaben kananan hukumomin Kano
- Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 14 a Jihar Kogi
- Taho-mu-gamar motoci ta kashe mutum 15 a Borno
Kungiyar ta lura cewa Gwamna Bello wanda za a ci moriyarsa kasancewarsa matashi, ya kuma kasance mutum wanda ba ya da kabilanci kuma hakan zai sa ya iya jagorantar kasar nan zuwa tudun tsira.
Bello, wanda a yanzu hake yake cikin wa’adinsa na biyu, ya kasance daya daga cikin matasan gwamnonin Najeriya wanda ya cika shekaru arba’in a shekarar 2015.
Kungiyar ta yi barazanar maka Gwamnan a gaban Kotu muddin ya ki amincewa da bukatarta ta tsayawa takarar shugabancin kasar nan a babban zabe mai zuwa.
“Muna farin cikin kara muryoyinmu a kai saboda mun san cewa mutane da dama sun nemi Yahaya Bello ya tsaya takarar Shugaban Kasa a 2023.”
“Muradin ’yan Najeriya na ganin kasar nan ta bunkasa ya yi daidai ta tsarin mutum tamkar Yahaya Bello, wanda dalilin haka ya sanya muka samu hujjar shiga sahun dimbin jama’ar da ke kira a gare shi da ya fito takarar Shugaban Kasa,” inji shi.
Ya ce kasancewar Bello yana da ’yancin tsayawa takara kamar yadda kundin tsarin mulki ya yi tanadi, hakan ya kara mana karfin gwiwar rokonsa da ya nemi kujerar shugabancin kasar nan.
Ya kara da cewa, ’yan Najeriya da dama suna rokon gwamnan da ya nemi kujerar Shugaban Kasar ne bisa la’akari da cancantarsa.