Kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban Kasa ta tabbatar da cewa Bola Tinubu ne ya lashe sakamakon zaben da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairun da ta gabata.
Alkalan kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Haruna Tsammani ne ya tabbatar da haka bayan ya je hukuncin karshe a zaman kotun na ranar Laraba.
- Kotu ta yi watsi da da’awar Atiku cewa Tinubu dan kasar Guinea ne
- Jam’iyyar LP ta yi watsi da hukuncin kotu kan zaben Shugaban Kasa
Kotun ta kuma ce Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi daidai da ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben.
A cewar kotun, wadanda suka shigar da karar sun gaza gabatar da gamsassun hujjojin da za su tabbatar da da’awarsu.
Mai Shari’a Tsammani ya ce, “Hujjojin da da masu shigar da kara suka gabatar da kwarara ba ne. A kan haka, ina tabbatar da nasarar da Bola Ahmed Tinubu ya samu a matsayin sahihin zababben Shugaban Najeriya.”
Kotun ta kuma yi fatali da hujjoji 37 da shaidu suka gabatar a gabanta.