✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yi watsi da da’awar Atiku cewa Tinubu dan kasar Guinea ne

Kotu ta ce zargin na Atiku ba shi da tushe ballantana makama

Kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban Kasa ta yi fatali da da’awar dan takarar jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar, kan cewa Shugaba Bola Tinubu ba dan Najeriya ba ne.

Atiku ya kuma zargi Tinubu da cewa ya taba yib harkallar miyagun kwayoyi a kasashen waje a shekarun baya.

Da take yanke hukunci a kan bukatar neman soke cancantar Atiku, kotun karkashin Mai Shari’a Moses Ugo, ya ce da’awar Atiku ba ta da tushe ballantana makama.

Atiku ya kuma roki a hana Tinubu takarar Shugaban Kasa saboda an taba kwace masa Dalar Amurka 460,000 domin a wanke shi daga zargin badakalar kwayoyi a wata kotun Arewacin birnin Illinois na Amurka.

Ya kuma yi zargin cewa Tinubu bai bayyana a jikin fom din da ya cike ya mayar wa INEC cewa yana da takardar shaidar zama ɗan Najeriya da ta kasar Guinea ba.