Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Mista Fayemi zai fito takarar shugaban kasa ne karkashin inuwar a Jam’iyyar APC, mai mulki, wadda za ta gudanar da zaben fitar da dan takarar shugaban kasarta a ranakun 30 da 31 ga watan Mayu da kuma 1 ga watan Yuni, 2022.
- Sojoji sun tsere bayan harin ISWAP a Chibok
- Dan Abiola ya bukaci Buhari ya binciki ‘yadda aka kashe mahaifinsa’
Da yake sanar da aniyar tasa a Abuja ranar Laraba, Fayemi ya yi alkawarin kawo shugabanci nagari da kma tabbatar da hadin kai idan aka zabe shi shugaban kasa a babban zaben na 2023.
A halin yanzu, Fayemi ya shiga jerin masu zawarcin kujerar shugaban kasa a jam’iyyar APC da suka hada da Mataimkain Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo; da Uban Jam’iyyar ta Kasa, Bola Tinubu da kuma Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.
Sauran sun hada da Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello; Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi; da tsohon Gwamnan Jihar Imo, Santa Rochas Okorocha.