✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Kano ta Kudu ta zabi Alhassan Rurum magajin Ganduje

Gamayyar 'yan asalin shiyyar sun bukaci samun kaso mai tsoka a siyasar Kano.

Gamayyar Kungiyar ‘Yan Asalin Yankin Kano ta Kudu (KSCCF), sun amince tare da zabar Alhassan Rurum a matsayin wanda zai maye gurbin gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a 2023.

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da mataimakin kungiyar ya fitar a ranar Lahadi, a madadin shugabanta Sanata Masud El-Jibrin Doguwa.

A cewar tsohon Sanatan Kano ta Kudu, Alhaji Musa Salihu, ya ce Kano ta Kudu ta cancanci kaso mai tsoka a siyasar Kano.

Salihu, ya ce Kano ta Kudu ba ta samu damar samar da gwamna a jihar ba tun daga 1992 kawo yanzu.

“Kano ta Kudu tana da manyan kananan hukumomi 16 a Jihar Kano.

“Kano ta Arewa da Kano ta Tsakiya sun samar da gwamnoni. A 2023 ya kamata a mayar da mukamin gwamna zuwa Kano ta Kudu.

Salihu, ya ce Kano ta Kudu na da muhimmiyar rawar da za ta taka wajen gina jihar Kano, inda ya ce yankin zai duk abin da ya kamata don tabbatar da cikar wannan manufa.

Ya kara da cewa, “Don haka muna goyon bayan Alhassan Rurum a matsayin gwamna a 2023 domin ya gaji gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

“Kuma mun zabi Honarabil Kawu Sumaila ya zama dan takarar Sanatan Kano ta Kudu da Honarabil Alhassan Ado Doguwa a matsayin dan takarar majalisar Tudun Wada/Doguwa domin ya samu damar zama kakakin majalisar.”

Gamayyar kungiyar ta ce nan ba da jimawa ba za ta kira taron masu ruwa da tsaki don bayyana matsayarsu kan ‘yan takarkarun da suka zaba.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Farfesa Abdu Salihi, Farfesa Isa Yahaya Bunkure, Galadiman Karaye, Alh. Surajo Garba Karaye, AIG Zarewa, Dokta Aisha Isyaku Kiru.

Ragowar sun hadar da Honarabil Alhassan Abubakar Tsohon Kakakin KNHA, Honarabil Abdullahi Maraya Kakakin KNHA, Limamai da Malamai daga Kano ta Kudu da lima kungiyoyin dalibai da dai sauransu.

Wakilin Aminiya ya ruwaito cewa, kungiyar ta kuma amince da Kawu Sumaila a matsayin wanda zai wakilci Kano ta Kudu a Majalisar Datijjai, sai kuma Alhassan Ado Doguwa ya sake zama dan majalisa mai wakiltar Tudun Wada da Doguwa.

Alhassan Rurum ya kasance tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano a wa’adin Ganduje na farko, inda a halin yanzu dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Rano, Kibiya da Bunkure kuma Shugaban Kwamitin fansho na majalisar.