Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce har yanzu yana ta kokarin neman wanda zai rufa masa baya a matsayin Mataimaki a zaben 2023 mai zuwa.
Ya bayyana haka ne a Abuja ranar Lahadi, lokacin da yake jawabi yayin bikin kaddamar da wani littafi don taya Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, murnar cika shekara 60 a duniya.
- NAJERIYA A YAU: ‘Yadda aka kwakule min idanu na da wuka’
- Mun yi wa mambobi miliyan 2 rajista a Borno — NNPP
Ana sa rana Tinubu zai ayyana sunan Mataimakin nasa nan da ranar 15 ga watan Yuli, lokacin da wa’adin da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ba jam’iyyu zai cika.
Wanda zai zaba dai shi ne zai maye gurbin Kabiru Ibrahim Masari, dan takarar wucin-gadin da ya zaba a kwanakin baya.
Tinubu ya kuma jinjina wa Kakakin Majalisar, wanda ya ce ya taimaka wajen bunkasa mulkin Dimokuradiyya a Najeriya kuma ya zama kyakkyawan abin koyi.
“Zan iya ganin Mataimakinka, Ahmed Idris Wase shi ma yana zaune a nan, wannan alama ce ta hadin kai da amintaka. Kun yi kokari. Ni ma zan dage na yi koyi da ku saboda har yanzu ina kan neman wanda zai min Mataimaki,” inji Tinubu.
Ya ce tun da dadewa alamun shugabanci suka bayyana a tare da Gbajabiamila, wadanda shi bai ma san yana da su ba.
Da yake nasa jawabin, Kakakin Majalisar ta Wakilai ya roki Tinubun ya ba shi damar taya shi lalubo wanda zai yi masa Mataimakin.
Ya yi alkawarin zabo masa dan takarar da ba zai yi da-na-sani a kan shi ba.
A bangaren littafin kuwa, Gbajabiamila ya ce ba wai kawai a kan shi aka rubuta ba, sadaukarwa ce ga duk wadanda suka taimaka masa ya kai matsayin da yake kai yanzu, musamman Tinubun.