Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce a makon farko na watan Oktoba mai kamawa ake sa ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2023 da ya kai Naira tiriliyan 19.76.
Ya ce matukar ba a sami canjin tsare-tsare ba, Shugaban zai gabatar da daftarin kasafin wanda shi ne zai kasance na karshe a wa’adin mulkinsa, a gaban zauren Majalisar Dokoki ta Kasa.
Gwamnatin Tarayya dai ta tsara kashe Naira tiriliyan 19.76 kamar yadda yake kunshe a daftarin kashe kudade na matsakaicin zango (MTEF) wanda aka gabatar wa majalisar a kwanakin baya.
Gbajabiamila ya bayyana haka ne ranar Laraba a Abuja, lokacin da ya kammala duba aikin yin kwaskwarima ga ginin harabar Majalisar Dokokin da ake yi.
Ana dai sa ran kammala gyaran ne nan da watan Agustan badi, kodayake ya roki masu aikin da su gaggauta kammala shi a kan lokaci sannan su yi mai inganci.
Femi ya ce, “Za mu yi alfaharin samun zauren majalisa da ya dace da kowanne iri a fadin duniya, kuma ya zuwa yanzu, na gamsu da yadda aikin ke tafiya.
“Ina kira ga ’yan kwangila da su dada jajircewa, duk da ma dai ba mu za mu ci gajiyar wannan aikin ba, sai majalisa ta gaba, saboda za a shafe kusan shekara daya nan gaba kafin a kammala shi,” inji Femi.
Shugaban ya kuma ce akwai yiwuwar a rantsar da majalisa ta 10 a wajen da ta yanzu take zama na wucin-gadi, in dai ba ’yan kwangilar sun yi kokarin kammala shi kafin cikar wa’adin da aka debar musu ba.