Kungiyar kabilar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo, ta ce dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, na bata lokacinsa ne kawai game da takarar da yake yi.
Babban Sakataren kungiyar, Mazi Okechukwu Isiguzoro, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ranar Juma’a.
Wike da Ortom sun kalubanci Buhari ya fallasa gwamnonin da ke sace kudaden kananan hukumomi
Aisha Buhari ta janye karar dalibin da ya tsokane ta
Isiguzoro ya ce, Atiku na girbar abin da ya shuka wa tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ne a 2015.
“Alhaki ne ke bibiyar Atiku Abubakar sakamakon sanyawa da ya yi wasu gwamnoni suka juya wa Jonathan baya wajen sake zaben sa a 2015.
“Ya hada kai da Jam’iyyar ACN a wancan lokaci karkashin Tinubu sa CPC karkashin Muhammadu Buhari sannan ANPP a karkashin Ogbonnaya Onu….,” inji shi.
Ya kara da cewa, a wancan lokaci Atiku ya samu nasarar sarrafa tsoffin gwamnonin da suka hada da Chibuike Amaechi da Rabiu Kwankwanso da Aliyu Wamakko da Abdulfatah Ahmed da kuma Murtala Nyako, suka juya wa jam’iyyarsu ta PDP baya.
Ya ce, ga shi yanzu rayuwa ta juya masa, yana girban abin da ya shuka, “Gara ma ya bar bata lokacinsa da kudinsa,” dangane da neman shugabancin kasar, inji Isiguzoro.