Gwamnonin Arewacin Najeriya 19 sun bayyana tsarin karba-karba a kujerar Shugaban Kasa a matsayin abin da ba ya cikin Kundin Tsarin Mulki.
Sun bayyana hakan ne a karshen taron da suka gudanar ranar Litinin a Kaduna, yayin da suke mayar da martani ga takwarorinsu na Kudu wadanda suka tsaya kai da fata cewa dole Shugaban Kasa mai zuwa ya fito daga yankinsu.
- An gurfanar da mutum 10 a gaban kotu kan kisan Fulani 27 a Jos
- Direbobin dakon mai na barazanar shiga yajin aiki
A wani taro da suka gudanar a Legas a kwanakin baya, Gwamnonin Kudun sun bukaci dole mulki ya koma yankinsu idan Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa a 2023.
To sai dai a karshen taronsu na Kaduna, Gwamnonin na Arewa sun ce ko da yake akwai wasu daga cikinsu da suka nuna goyon bayan mulkin ya koma Kudu don amfanin hadin kan kasa, matsayin da takwarorin nasu na Kudu suka dauka ba abu ba ne da za su lamunta.
Da yake karanta matsayinsu, Shugaban Gwamnonin, kuma Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya ce, “Matsayin da suka dauka ya ci karo da tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima.
“Kundin dai ya tanadi cewa dole zababben Shugaban Kasa ya sami kaso 25 cikin 100 na kuri’in da aka kada a a jihohi biyu bisa uku na Najeriya, idan bukatar gudanar da zagaye na biyu ta taso a zaben,” inji Lalong.