✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: Atiku ya fara bin ’yan takarar da ya kayar a PDP gida-gida

Ya dai sha alwashin hade kan jam’iyyar waje daya don ya kai ga nasara

Dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya fara bin wadanda ya kayar a zaben fid da gwanin jam’iyyar gida-gida don neman su yi aiki tare.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Atiku ya kai ziyarar ce ga Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, a gidansa da ke Abuja ranar Litinin.

Ziyarar na zuwa ne kwana daya bayan dan takarar ya ziyarci Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, wanda da ya janye masa takara a zaben fid da gwanin jam’iyyar na ranar Asabar.

A shafinsa na Twitter dai Atiku ya ce: ziyarar na daga cikin kokarinsa na tafiya tare da kowa a jam’iyyar.

Ya ce, “A ci gaba da yunkurinmu na kawo kowa tare da tabbatar da cewa PDP ta zama tsintsiya madaurinki daya, a yau [Litinin] na ziyarci Gwamna Nyesom Wike a gidansa da ke Abuja.

“Wannan abu ne da za mu ci gaba da yi,” kamar yadda dan takarar ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Daga bisani kuma ya sake ziyartar gidan tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma daya daga cikin wadanda suka nemi takarar, Anyim Pius Anyim.

Atiku dai ya samu nasara ne a zaben fid da gwanin na PDP da kuri’a 371, inda ya doke abokin karawarsa na kurkusa da shi a yawan kuri’a, wato Wike da ke da kuri’a 237.

A yayin jawabinsa dai bayan ya lashe zaben fid da gwanin, Atiku ya yi alkawarin yin aiki tare da sauran wadanda suka nemi takarar don ganin jam’iyyar ta kai ga gaci.