✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2023: APC ce za ta lashe zaben Gwamnan Sakkwato —Dingyadi

Ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da kwamitocin kula da kananan hukumomi na jihar.

Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Muhammad Maigari Dingyadi ya ce jam’iyyar APC ce za ta lashe zaben Jihar Sakkwato a 2023.

Ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da kwamitocin kula da kananan hukumomi na jihar, inda ya ce jam’iyyar ce za ta sake lashe zabe a Najeriya.

“Za mu ci gaba da jajircewa kuma ba za mu taba yanke kauna ba, in sha’a Allahu, APC za ta lashe zaben gwamna a 2023.”

Dingyadi, ya yaba wa shugabancin jam’iyyar a jihar, saboda samar da ingantaccen shugabanci.

Ya yaba wa jagoran APC na jihar, Sanata Aliyu Wamakko da sadaukar da kansa ga jama’ar jihar inda ya ce nasarorin da jam’iyyar ta samu a jihar, ta samu ne saboda nagarta da jajircewarsa.

Wamakko, wanda ke wakiltar gundumar Sanatan Sokoto ta Arewa, ya ce, an sake nada su shugabannin rikon kwayar ne saboda rashin samun shugsbanci nagari da jam’iyyar ta yi fama da shi a baya.

Ya kuma bayar da tabbacin ci gaba da kokarin ganin cewa, jam’iyyar ta bunkasa daga mataki zuwa mataki.