✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: An saya wa Tinubu fom din takarar APC kan miliyan N100m

Magoya bayan shi ne suka saya masa saboda ya tafi Umara

A ranar Juma’a mai neman takarar Shugaban Kasa kuma jigo a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yanki takardar tsayawa takarar a kan kudi Naira miliyan 100 a Abuja.

Magoya bayan Tinubun ne suka wakilce shi wajen sayen fom din kasancewar ya tafi Umarah a kasa mai tsarki.

Kawo yanzu, wadanda suka sayi takardar takarar Shugaban Kasa a karkashin tutar APC sun hada da; Minista a Ma’aikatar Ilimi, Emeka Nawjiuba, Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi, Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi da sauransu.

Duk da dai APC ba ta fito ta nuna shiyyar da za ta mika wa takarar Shugaban Kasar ba, amma galibin wadanda suka sayi fom ya zuwa yanzu daga Kudancin kasar nan suka fito.

Kafin babban taron APC da ya gudana watannin baya, an ji Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya ce, APC ba ta dauki matsaya game da shiyyar da za ta mika wa takarar ba.

Sai dai yadda aka yi rabon mukamai a jam’iyyar ta APC wata ’yar manuniya ce dangane da shiyyar da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar zai fito.

Ranar uku ga watan Yuni mai zuwa ce dai ranar da Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) ta tsayar a matsayin ranar karshe a kan kowace jam’iyya ta tabbatar da ta mika sunayen ’yan takararta.