An nada tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Farfesa Hafizu Abubakar, a matsayin Shugaban Kungiyar Yakin Neman Zaben Yemi Osinbajo (OSO) a matsayin Shugaban Kasa a 2023.
An dai tabbatar da nadin nasa ne tare da wasu shugabannin tafiyar yayin wani taron kungiyar da ya gudana a Kano ranar Asabar.
- PDP ga Ganduje: Kashe N525m don kawata gadar Kofar Ruwa almubazzaranci ne
- Ya hada kai da abokansa wajen guntule kan budurwarsa don yin tsafi
Farfesa Hafizu dai shi ne Mataimakin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje daga shekarar 2015 zuwa 2018.
Taron dai ya samu halartar kungiyoyin magoya bayan Mataimakin Shugaban Kasar da suka fito daga sassa daban-daban na Najeriya.
Da yake jawabi yayin taron, Daraktan Tsare-tsare na kungiyar, Bashir Suwaid, ya ce akalla kungiyoyin da ke goyon bayan Osinbajo sama da 45 ne suka halarci taron.
Kazalika, taron ya kuma zabi shugabanni daga dukkan shiyyoyin siyasa guda shida na kasar nan.
“Akwai kungiyoyi 45 da suka zo daga sassa daban-daban na kasar nan domin kaddamar da jagororin kungiyar OSO a hukumance, inda tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Farfesa Hafizu Abubakar, a matsayin jagora,” inji Bashir Suwaid.
Sauran mukaman jagororin kungiyar sun hada da Daraktan Tsare-tsare da Mai ba da Shawara a Bangaren Shari’a da Daraktan Kudi da na Wayar da Kan Jama’a da na Mulki da kuma na Yada Labarai da dai sauransu.