Kungiyar tallata takarar Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, don zama Shugaban Kasa a 2023 (YBN) ta ce ta kaddamar da sabbin rassa har guda uku don fadada tafiyar.
A cewar shugaban kungiyar, Abdul Muhammad wanda aka fi sani da Mai Kwashewa, yanzu rassan kungiyar sun zama guda 10 ke nan.
- Mun kusa kammala zagaye na farko na yakin Ukraine – Rasha
- 2023: Babu adalci a tsarin karba karba – Sheikh Jingir
Sabbin rassan da aka kaddamar a Kano dai sun hada da reshen dalibai da na masu bukata ta musamman da kuma na ’yan siyaya tun daga tushe.
A cewar Mai Kwashewa, manufar YBN ita ce yin aiki tukuru wajen ganin Gwamna Yahaya Bello ya cim ma muradalinsa a na ciyar da Najeriya gaba.
Ya ce dan takarar nasu zai bunkasa tattalin arziki ya samar da ingantaccen tsaro da nagartaccen ilimi da a harkar lafiya muddin ya zaman Shugaban Najeriya a zabe mai zuwa.
Da yake nasa jawabin, Gwamna Yahaya Bello, wanda Shugaban Ma’aikatan Fadarsa, Jamiu Asuku, ya wakilta, ya ce an kaddamar da sabbin rassan ne saboda muhimmancinsu a cikin al’umma.
Wakilan rassan da aka kaddamar dai sun nuna jin dadinsu, tare da alkawarin yin aiki tukuru wajen ganin manufar tasu ta tabbata.
Kusoshin gwamnati daga Jihar Kogi da manyan taurarin masana’antar shirya shirya finafinai ta Kannywood da sauran dimbin jama’a ne suka halarci taron kaddamarwar.
Aminiya ta rawaito cewa mutane daga sassa daban-daban na kasar nan ne suka halarci taron.