✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2022: Miyagun kwayoyi 8,387kg da mutane 1,078 NDLEA ta kama a Kano

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce Kilogram 8,386.733 na kwayoyi da mutane 1,078 ta kama a jihar Kano…

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce Kilogram 8,386.733 na kwayoyi da mutane 1,078 ta kama a jihar Kano a shekarar 2022.

Kwamandan hukumar na Kano, Abubakar Idris Ahmad ne ya bayyana hakan a taron shekara-shekara na manema labarai da hukumar ta shirya ofishinta da ke jihar ranar Alhamis.

Ya ce sun kama tabar wiwi kilogram 6,607.49kg, hodar Iblis gram 451, Kilogram 1,778.388 na haramtattun kwayoyi, da gram 402 na sauran haramtattun kayan maye.

“A bangaren masu ta’ammali da ita kuwa, mutane 172 muka gurfanar a gaban kotu, daga ciki kuma an daure 113, sai 126 da ba a kammala shari’un ba.

“Haka kuma fiye da wurare 82 da suka yi kaurin suna a shaye-shaye da fatucin kwaya a ciki da wajen Kano muka tarwatsa.”

Wuraren sun hada da Jakara, Filin Wasa na Ahmed Musa, Kulob din Bubble Plus, gidan kallo na Dawanau, da kulob din Zaro, da gidan abincin 360.

Sauran sun hada da gidan kallon Eldorado, Kulob din Dan Nagari, filin wasa na Sani Abacha, filin wasa na Sabon Gari, Dorayi Karshen Waya, gidan abinci na Red, da otel din River Bird da sauransu.

“Banagren gonakin tabar wiwi kuwa biyar muka gano a kananan hukumomin Dawakin Kudu, Bichi, Danbatta, Gwarzo da Nassarawa, kuma mun lalata su”, in ji shi.

Ahmad ya kara da cewa, a kokarinta na dakile matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyin, Hukumar ta dora wa wani sashi na jami’anta alhakin wayar da kan jama’a, tare da bayar da shawarwari don gyaran halin wadanda suka yi nisa a shaye-shayen.

Ya kuma ce makarantu 150 ne suka ci gajiyar bitocin illolin muggan kwayoyin, sannan sama da masu shanta 1,844 sun samu kulawa da kuma gyaran hali daga hukumar.

“Baya ga haka, Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya-Janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya ya amince da kara bude ofisosin hukumar a Rano da Tudun Wada, da kuma samar da jami ’i a karamar hukumar Gaya.

“Dalilin hakan bai wuce don ayyukanmu su watsu zuwa kowane lungu da sakon jihar ba, da kuma kawo karshen fatauci da shan miyagun kwayoyi da suka yi wa jihar katutu”, in ji Ahmad.