Kungiyar nan mai fafutukar kare hakkokin Musulmi a Najeriya (MURIC) ta bukaci gwamnatin tarayya da ta sake salon magance ta’addancin Boko Haram a kasar.
Shugaban kungiyar MURIC Farfesa Ishaq Akintola ne ya yi kiran ranar Asabar a sakonsa na sabuwar shekara.
- Ronaldo ya zama dan kwallo na biyu mafi zira kwallaye a tarihi
- ’Yan ta’adda sun yi wa mafarauci yankan rago a Abuja
- Coronavirus ta kashe mutum 9 a Najeriya, 917 sun kamu
Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta gabatar da hakkokin musulmin Najeriya wanda ke da alaka da karfafa wa mabiya addinin da kuma bayyana abubuwan da ke kawo rikici wanda ba ya cikin tsarin musulunci da ‘yancin musulmin Najeriya.
“Najeriya tana bikin ranar farko wanda ta yi daidai da ranar Juma’a ta kalandar Miladiyya 1 ga watan Janairu 2021.
“Wasu jama’a da yawa a duniya a shekarar da ta gabata ta zo da bazata ta inda ba za a taba manta ta ba.
“Shekarar 2020 ta zo da annobar COVID-19 da kuma kakaba dokar kulle sannan ga fargabar zanga-zangar #EndSARS.
“Shekarar 2020 ta zo da rudani a Najeriya, yayin da ake fuskantar kalubale na rashin tsaro da kuma hare-haren ’yan Boko Haram ga karuwar barayin shanu da kuma masu garkuwa da jama’a don neman kudin fansa, duk ’yan Najeriya sun fuskanci wadannan kalubalen da wanda ya dade da kuma sabbin rikice-rikicen da ake fuskanta.”
“A yayin da sojojin Najeriya ke yakar mayakan Boko Haram a filin da-ga akwai bukatar a yi ganawar sasantawa da shugabannin musulmi da kungiyoyi a kasa,” inji Farfesa Ishaq.