✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2019: Yakamata mu hankalta

Babu shakka zaben shekarar 2019 zabe ne da talakawa masu hankali za su share wa kansu hawaye ta hanyar zaben managartan mutane zakakurai, wadanda suke…

Babu shakka zaben shekarar 2019 zabe ne da talakawa masu hankali za su share wa kansu hawaye ta hanyar zaben managartan mutane zakakurai, wadanda suke da kishin gaske gami da tashi-tsaye da dukanin karfinsu wajen sama wa yankin da suke wakilta duk wani nau’i na ci gaba.

Ga duk mai bibiyar lamurran siyasar kasar nan yana ganin yadda abubuwa ke wakana a dukan sassan kasar nan,  dangane da yadda kusan kowane wakili yake gudanar da aikin da aka tura shi majalisa da kuma yanayin yadda yake rike da jama’arsa amma da mutuntawa ko akasin haka.

Shakka babu duk da irin mawuyacin halin da ake ciki a kasar nan akwai zakakuran wakilai da koyaushe ba sa gajiyawa wajen sauraron korafe- korafen jama’ar da suke wakilta tare da taimaka musu daidai gwargwadon iyawarsu.

A hannu daya kuma akwai wadanda suka yi rashin dacen zabar wakili, ma’ana suka yi zaben tumun-dare, sakamakon guguwar canjin da ta kada a shekarar 2015.

Zahiri, masarautar Gumel na daya daga cikin yankin da sakamakon zaben 2015 ya bar su da tagumi, sakamakon zaben wakilan da kansu da iyalansu kawai suka sani. Ba su da aiki sai tsabagen surutu kamar sun hadiyi cakwaikwaiwa!

Wannan dalili ne ya sa al’ummar yankin masarautar Gumel laluben wadanda za su maye gurbin irin wadancan lusarai. Kuma daya ne daga cikin dalilan shawartar zakakurin matashi Murtala Habu Chari  ya fito takarar wakiltarsu a Majalisar Wakilai dangane da lura da yadda ba ya da kowane irin mukami na siyasa amma koyaushe hidimta wa al’ummarsa ne a gabansa wanda hakan ne ya sa ya gina masana’antun da shi kansa bai san adadin mutanen da ke cin abinci a karkashinsu ba.

Shakka babu idan har wannan abu ya tabbata to masarautar za ta zamo daya daga cikin zakaran gwajin dafin da za ta yi gogayya da kowane yanki a kasar nan da kuma alfahari da wakilcin da ake yi musu. Ina fata kowane yanki za su duba hazikan matasa daga cikinsu. 

Matasa masu jini a jika da sanin ya kamata domin maye guraben wadanda ba abin da suka sani sai barci a majalisa da kuma wadanda suka kware a fannin yaudara da surutun tsiya!

Allah Ya yi mana jagora, Ya kuma azurtamu da shugabanni nagari masu kaunarmu da gaske amin.

Kabiru Maigari Gumel 08028480098 ko 08065642652.