✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2019: Tawagar Kwankwasiyya ta fara tuntubar mutane a Kurosriba

A Jumu’ar da ta gabata ce, kungiyar Kwankwasiyya ziyarci garin Kalaba, fadar Gwamnatin Jihar Kurosriba da nufin tuntuba da kuma ganawa da magoya bayanta da…

A Jumu’ar da ta gabata ce, kungiyar Kwankwasiyya ziyarci garin Kalaba, fadar Gwamnatin Jihar Kurosriba da nufin tuntuba da kuma ganawa da magoya bayanta da ke daukacin kananan hukumomi 18 na jihar, karkashin jagorancin tsohon Minista, Sanata Ahmed Garba Bichi. Sai dai tawagar ta gamu da korafe-korafe daga wasu ’ya’yan kungiyar na jihar.

Wakilin karamar Hukumar Boki Egam Agor, a jawabinsa, ya fara ne da korafin cewa shi bai ga wakilin Kwamkwasiyya a jihar ba. “Na lura jagoran Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a tawagarsa babu wakili daya daga cikin jihohin Kudanci, wanda kamata ya yi a cikin mukarraban shugaban tawagar tafiyar a ce an samu mutum daya a ciki da ya fito daga Kudu Maso Kudu da kuma Kudu Maso Gabas amma na ga dukkaninku ’yan Arewa ne,” inji shi.

Shi ma wani da ya halarci zauren tuntubar mai suna Alhaji Magaji, ya nuna shakku a kan matukar ana so a cin ma nasara a Kwankwasiyya. Ya ce sai an kauce wa abin da ya faru lokacin da aka yi guguwar canji, ta yadda idanun wasu ’yan siyasa ya makance, a lokacin da ake kokarin kawar da jam’iyyar PDP daga mulki ko ta wane hali; inda ya ce a karshe aka yi kitso da kwarkwata. Ya jawo hankalin cewa a wannan tafiya sai an yi hattara, gudun kada a koma gidan jiya. Ya ba da shawarar cewa a tafi da kowa da kowa.

An kaddamar da shugabanni da kuma jagorori a matakin jiha da kuma na kananan hukumomi da za suci gaba da yada manufar Kwankwasiya a kananan hukumominsu kana kuma su hada kansu ba tare da nuna wani banbanci ba.

Wakilinmu ya tambayi shugaban tawagar, Ahmed Garba Bichi game da makasudin zuwansu jihar sai ya ce: “Mun shigo Kalaba domin mu isar da sako na takara, wadda ba tun yau aka fara ta ba, tun daga 2015. Yanzu kuma ga shi Allah Ya kawo mu, muna kusantar shekara ta 2019. Mun zo Kurosriba domin tuntuba daga lokaci zuwa lokaci a kan takarar shugaba, uban tafiyarmu, Injiiya Rabi’u Musa Kwankwaso,” inji shi.

Ya ce wannan sakon ne suka zo isarwaga masu ruwa da tsaki na wannan jihar. “Domin a da suna tafiya daban-daban a wannan tafiya ta Kwankwasiya. Shi ya sa muka umarce su da su  hade tafiyar wuri guda, su dunkule wuri guda, su rika yin taruka bayan mun tafi; ta yadda za su rika yim magana da murya daya. Abin zai fi mana sauki, su ma zai yi musu sauki. Tafiyar za ta yi mana sauki yayin da suka dunkule wuri daya.”