✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

2019: Buhari ne zai lashe zabe a Arewa maso Gabas – Gwamnan Borno

Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno shi ne shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, ya bayyana wa manema labarai bayan taron Shiyyar Arewa maso Gabas na Jam’iyyar…

Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno shi ne shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, ya bayyana wa manema labarai bayan taron Shiyyar Arewa maso Gabas na Jam’iyyar APC a Bauchi cewa lallai Shugaba Buhari ne zai lashe zabe a shiyyar duk da cewa dan takarar PDP ya fito ne daga shiyyar.

 

Kasancewar dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP ya fito ne daga shiyyar Arewa maso Gabas ba ka gani zai rage wa APC yawan kuri’a da za ta samu a shiyyar?

Kamar yadda muke fadi kullum ita siyasa a karkara ake yinta kuma a rumfar zabe ake kada kuri’a, sannan wadannan yankunan karkara suna da abubuwa da dama da suka addabe su. Suna fama da matsaloli da suke ci musu tuwo a kwarya. Shekara hudu da suka wuce mu da ke zaune a wannan yanki na Arewa maso Gabas mun san halin taskun da muke ciki, amma a yau mu muka fi kowace shiyya morar gwamnatin Shugaba Buhari. In ka dubi irin mukaman da aka nada a Gwamnatin Tarayya namu ne mafi yawa. Ka dubi matsalar tsaro da ke addabar wannan shiyyar, Buhari ya yi rawar gani wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Ka dauki aikin samar da wutar lantarki na Mambilla kawai ya isa ’yan Najeriya musamman mazauna wannan shiyya su goya masa baya, saboda muhimmancinsa, domin zai gina tattalin arziki da walwalar jama’a ya sauyin rayuwar al’umma. Saboda haka shiyyar Arewa maso Gabas shiyya ce ta masoya Shugaba Buhari, kuma na yi imani da Allah, in Allah Ya yi nufi mutanen shiyyar za su goyi bayan Shugaba Buhari a zaben 2019. Muna yi masa fatan alheri muna kuma yi wa dan takarar PDP fatan alheri, amma siyasa abu ce da ke kunshe da warware matsalolin al’umma. Buhari ya yi yunkuri mai karfi don warware matsalolin da suka dabaibaye shiyyar. A shekarar 2015, Borno mu ne muka bai wa Buhari kashi 97.3 na yawan kuri’un da muka kada, kuma a 2019 na yi imani cewa za mu sake ba shi wadannan kuri’u da ikon Allah.

Yanzu al’amura sun sauya, abin ya wuce daga inda mutum ya fito ko daga yankin da ya fito. Abin da ake lura shi ne me mutum ya yi mana ta fuskar kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Wane kokari ya yi don farfado da talaka da ba shi mutunci da daraja, in ka duba sai ka ga Buhari ya yi namijin kokari a wadannan abubuwa. Ya karbi kasar nan lokacin da komai ya lalace, kuma yana da wahala a gyara kasar cikin shekara 4. Ina shaida muku a yau ko a fagen tsaro muna da kalubale, akwai abubuwan da suka dame mu, amma in ka kwatanta halin da muke ciki shekara hudu baya da yadda ake yau, dole ka yaba masa, saboda mun samu gagarumin sauyi ta fuskar tsaro. Bari in ba ku misali, a baya kananan hukumomi 20 zuwa 22 a Jihar Borno da kanana hukumomi biyar a Jihar Adamawa da kananan hukumomi biyu a Jihar Yobe suna karkashin ikon Boko Haram ne. Muna cikin matsaloli ba shakka, amma in ka dubi jiya ka ga yau dole ka gode wa Allah kasancewa an samu matukar ci gaba kuma in Allah Ya yarda za mu kara hada karfi da karfe mu ga cewa mun kawo maslaha.

Ana zargin cewa mutane ba sa fitowa su fada wa sojoji maboyar wadannan mutane?

Daga ina ne aka fara jami’an tsaro na sa kai? Daga ina aka turo su? Ai cibilian JTF daga Borno ya taso da mutanen Borno ba sa ba da hadin gwiwa ba za a ce yaranmu su je su mutu a filin daga ba.

Kuna tuntubar kasashe makwabta kan wannan batu?

Wannan abin  Gwamnatin Tarayya ne kuma yanzu haka Ministan Tsaro ya je kasar Chadi. Na yi imani ya je tattaunawa ce a kan Boko Haram amma ba ni da cikakkakiyar masaniyar abin da ya kai shi. Abin da zan ce ba za a rasa sha’anin tsaro ba cikin tafiyar da ya yi ba.

Me kuke fada wa al’umma?

Allah Ya ba mu hadin kai. Allah Ya ba mu zaman lafiya domin zaman lafiya shi ne komai.

Ga shi har yanzu kun gaza shawo kan matsalolin cikin gida na Jam’iyyar APC, wadansu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar suna ta korafi har yanzu, kuma wadansu sun ki zuwa taron sasantawar a wasu jihohi saboda suna da matsaloli da gwamnoninsu, me za ka ce?

Siyasa a yanzu tamkar yaki ce, ba abar wasa ba ce, ba na so in sa wasa a cikin hidimar siyasa, don neman mulki ba abin wasa ba ne. Amma a karshe an sani cewa shugaba guda daya za a zaba, mutum 20 ko 30 ko fiye na iya fitowa takara suna neman mukamin gwamna ko sanata amma a karshe mutum guda kawai zai kasance dan takarar da jam’iyya za ta tsayar. Mu dai muna iya kokarinmu mu ga an sasanta domin babu wanda zai ce shi kadai zai iya yin gwamna, dole sai an dafa masa. Muna bukatar junanmu dukanmu domin mu karfafa tafiyarmu mu karfafa jam’iyyarmu. Za mu isa ga dukan wadanda ke da korafi domin ba makawa mu sasanta.