Kwamitin Duban Wata (NMSC) na Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ya ce ba a ga watan Muharram na Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1442 ba.
Kwamitin wanda tun da farko ya bukaci al’umma Musulmi da su nemi jinjirin watan Muharram 1442 Bayan Hijira a ranar Laraba 19 ga watan Agusta 2020, wanda shi ne 29 ga watan Zhul Hajji, ya ce bai samu rahoton ganin watan ba a kasar.
“Zuwa karfe 7:38 na dare babu rahoton ganin sabon wata a Najeriya, saboda haka Mai Alfarma Sarkin Musulmi ba ayyana Alhamis a matsayin 1 ga watan Muharram [1442] ba.
“Don hakan gobe (Alhamis) ita ce 30 ga watan Zhul Hajji 1441, sannan Juma’a za ta zama 1 ga watan Muharram na Sabuwar Shekarar (Musulunci), inji Sheikh Salihu Muhammad Ya’qub, Jami’i a Kwamitin.
In za a iya tunawa Shugaban Kwamitin Harkokin Addinin Musulunci na Fadar Sarkin Musulmi, Wazirin Sakkawato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, a wata sanarwa ya ce Laraba 19 ga Agusta, 2020 ita ce 29 ga Zhul Hajjin 1441 Hijiriyya, ranar duban farko na watan Muharram mai kamawa.
Sanarwtar ta bukaci Musulmi da su kai “rahoton ganin watan ga sarakunan yankunansu domin su nasar da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar”.