✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɗalibai za su koma makaranta ranar Lahadi da Litinin – Gwamnatin Kano

Gwamnatin ta ayyana Litinin a matsayin ranar da ɗaliban jeka ka dawo za su koma makaranta.

Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa ɗaliban makarantun kwana na gwamnati da na masu zaman kansu za su koma makaranta a ranar Lahadi 6 ga watan Afrilu, 2025.

Wannan ya shafi makarantun firamare da sakandare domin ci gaba da zangon karatu na uku na shekarar 2024 zuwa 2025.

Ga ɗaliban makarantun jeka ka dawo kuwa, za su koma makaranta a ranar Litinin 7 ga wata. Afrilu, 2025.

Sanarwar da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, ya fitar, ta buƙaci iyaye da su kula da wannan rana domin tabbatar da cewa yara sun koma makaranta a kan lokaci.

Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dokta Ali Haruna Makoda, ya gargadi ɗalibai da su guji kawo miyagun abubuwa kamar wuƙa, reza ko ƙwayoyi zuwa makaranta.

Ya kuma ce gwamnati za ta ɗauki mataki a kan duk ɗalibin da ya ƙi bin wannan doka.

Ya ƙara da cewa bin doka da ƙa’ida na taimaka wa ɗalibai su samu nasara a karatunsu.