A safiyar Lahadi wasu bata-gari suka fasa gidan tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da ke garin Jos, Jihar Filato.
Jaridar Punch ta rawaito cewa bata-garin sun karya dokar hana fita da gwamnatin jihar ta saka, inda suka shiga fasa gine-ginen gwamnati domin neman kayan tallafin COVID-19.
- Ana zaman zullumi a Jos saboda #EndSARS
- Gwamnatin Filato ta sake dawo da dokar hana fita
- EndSARS: Gwamnatin Filato ta sassauta dokar hana fita
- Ba za mu bari Filato ta sake fadawa cikin rikici ba —Lalong
“Sun fasa gidan tsohon Shugaban Majalisar Waiklai, Dogara, sun farmaki duk wanda suka samu a gidan, ciki har da dan uwansa.
“Sun kwashe kayayyaki da dama daga ciki har da kayan laturoni, kujeru da sauran kayan amfanin gida”, inji wani ganau.
Wanda lamarin ya faru a kan idonsa, ya shaida wa manema labarai cewa-bata garin sun fasa gidan Dogara ne da misalin karfe 9 na safe.
Sai dai jami’an tsaro sun tarwatsa gungun bata-garin ta hanyar yin harbi a iska.