Tun bayan gabatar da wata muƙala mai tsawo da na yi tsakanin shekarar 2011 da 2012 kan ɓangarorin wayar salula, ban gushe ba ina ta samun saƙonni masu alaƙa da rubutun, wajen neman cikakkiyar muƙalar, ko neman shawara a kan wace irin waya za a saya, ko kuma me ya sa wayoyin salula wasu suke da ɗan karen tsada, wasu kuma da araha? Me ke kawo wannan bambancin farashi?
Amsa kan wace irin waya mai karatu zai saya, na sha maimaita ta a wannan shafi namu mai albarka, da ma saƙonnin Imel ko na Tes da nake aikawa ga galibin waɗanda suke min irin wannan tambaya.
Abin da ya rage ba mu amsa ba shi ne dalilan da ke sa wasu wayoyin salula ke da ɗan karen tsada, wasu kuma da araha.
Wannan, a taƙaice, shi ne abin da wannan muƙala tamu ke ƙunshe da shi in Allah Ya so.
Bunƙasar wayar Tsakanin jiya da yau Salula:
Ko shakka babu akwai bambanci mai girman gaske a tsakanin fasahar wayar salula a shekara 10 zuwa 20 da suka gabata da irin waɗanda muke amfani da su a zamanin yau.
A shekarun baya, kamfani mafi girma da tasiri a harkar salula a duniya shi ne Kamfanin Nokia. A yanzu ba a jin ɗuriyarsa.
A baya babbar manhajar salula da ake taƙama da ita – wanda duk cikan wayar salula, idan ba ita ba ce a kanta banza ce – ita ce babbar manhajar Symbian, wadda Kamfanin Nokia ne ya mallake ta a lokacin.
Duk sauran kamfanonin wayar salula na karɓar lasisi ne a wajensa don ɗora wannan babbar manhaja a wayarsu don samun kasuwa. A yanzu ba maganar wannan babbar manhajar ma ake ba.
Da yawa cikin samari ’yan bana-bakwai idan ba waɗanda suka samu labarinta a jami’o’i wajen karatu ba, ba su ma san ta ba.
Manyan manhajojin wayar salula da suke cin kasuwarsu yanzu su ne:Android, wadda Kamfanin Alphabet (ko Google) ya mallaka tare da bayar da lasisinsa ga sauran kamfanonin ƙera wayar salula da ke duniya.
Sai kuma babbar manhajar wayar salula mai suna iOS na Kamfanin Apple, wadda ke ɗauke kan manyan wayoyin salula da kusan suka fi kowace irin wayar salula tsada a duniya.
Haka abin yake a ɓangaren zahirin siffofin wayar salula, wajen buɗewa da rufewa, wajen kiran waya da amsa kira, wajen aika saƙonnin tes, wajen ɗora katin SIM.
Duk a yanzu sun zama tarihi. Wasu ne suka maye gurbinsu, suna kuma k ere su wajen inganci da girman jiki da tsawon lokacin amfani da kuma tsada.
Wayoyin zamanin jiya suna ɗauke ne da manhajojin wayar salula da ake ƙera ko gina da Java, ko waɗanda aka gina da C++, ko waɗanda aka gina da Python.
A yanzu ma ana gina manhojin wayar salula da waɗannan nau’o’in dabarun gina manhaja, amma bambancin da ke tsakani shi ne, waɗancan manhajojin na zamanin jiya, idan aka gina su aka ɗora su tun sa’ar da ake haɗa wayar, to, ba a iya sake ɗora wata manhaja kuma a kan wayar.
Amma a zamanin yau, muna da cibiyoyin manhajojin wayar salula a kan wayar; ka hau, ka duba manhajar da ta yi maka, ka saukar, sannan ka ɗora wa wayarka ta ci gaba da aiki.
Ba wannan kaɗai ba, idan kai ƙwararre a fannin gina manhajar wayar salula ne, kana iya amfani da wayarka wajen gina wata manhaja, sannan ka ɗora manhajar a kan wayar don amfani da ita kaitsaye.
Dangane da yanayi da hanyoyin sadarwa na rediyo ko Intanet ma, wayoyin zamanin yau sun sha bamban nesa ba kusa ba, idan aka kwatanta su da wayoyin salula na zamanin jiya.
A baya mafi girman waya wajen inganci da tsada takan taƙaitu ne da tsarin sadarwa na 3G.
Sauran duk ba su wuce wayoyi masu amfani da tsari da kuma ƙa’idar sadarwa na Karni na 2 (2G Network) ba.
Amma a yanzu, saboda saurin ci gaba a fannin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani, galibin wayoyin salula suna ɗauke ne kan tsari da ƙa’idar sadarwa na Karni na 4 (4G Network) da Karni na 5 (5G Network).
To duk me ya jawo wannan saurin ci gaba ne, cikin shekarun da ba su shige 15 ba zuwa 20, idan ma sun kai?
Manyan dalilan da suka kawo saurin yaɗuwa da bunƙasar inganci da yawaitar wayar salula da fasahar da ta dangance ta a duniya, suna da yawa.
Shahararru daga cikinsu sun haɗa da ingancin bincike a fannin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani da samuwar nau’o’in wayoyi daban-daban da yawaitar kamfanonin ƙera wayoyin salula da samuwar wayoyi masu farashi daban-daban da tilascin zamani wanda ke sa mutane mallakar wayoyin salula a wasu wuraren da fasahar ba ta kai ba da samuwar dokokin kula da harkokin sadarwa daga hukumomin ƙasashe daban-daban a duniya da sauran dalilai masu yawa da suka danganci waɗanda suka gabata.