✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɗan tsohon gwamnan Kaduna ya rasu a hatsarin mota

Rahotanni sun tabbatar da cewar matashin ya gamu da ajalinsa a wani hatsarin mota a Kaduna.

Faisal Ahmed Mohammed Makarfi, ɗan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Ahmed Mohammed Makarfi, ya rasu a hatsarin mota.

Ya rasu da yammacin ranar Asabar a wani mummunan hatsarin mota a Kaduna.

Wani daga cikin iyalinsa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar wa Aminiya rasuwar.

Iyalan tsohon gwamnan za su yi cikakken bayani.

 

Cikakken bayani na tafe…