Ana zargin wani ɗalibi da ke shekarar ƙarshe a jami’a da ƙona budurwarsa mai ɗauke da tsohon ciki a Jami’ar Fatakwal da ke Jihar Ribas.
Wanda ake zargin da budurwar tasa mai suna Cynthia Chukwundah, dukkansu ɗaliban ajin ƙarshe ne a jami’ar.
Ana zargin matashin ya ƙona Cynthia mai shekara 32 ne ta hanyar wata mata ruwan batir, daga bisani ta ce ga garinku nan.
Cynthia ta gamu da ajalinta ne bayan saurayinta Sunny Amadi ya yi mata wannan aika-aika a gidansu da ke layin Okoro unguwar China da ke Birnin Fatakwal.
- Sojoji sun kama mai garkuwa da mutane da bindigogi
- Muna tunanin sayar da matatun man Najeriya — NNPCL
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa “Abu kamar wasa suka fara cacar baki, wannan na faɗa wannan na mayar da martani kowa dai bai sanya musu baki ba, kowa kuma ya shiga ɗakinsa ya kwanta. Ƙarshe sai ya watsa mata wani sinadarin da ya ƙone ta kamar ƙunar wuta, ga ta ɗauke da tsohon ciki, ita da tsohon ciki da abin da ke cikin cikin suka mutu,” in ji majiyar.
Ya ce, “Bayan da saurayin ya yi wa Cynthia wannan aika-aika, ya sulale ya gudu, amma daga baya ’yan sanda suka kama shi a maɓoyarsa.
“Maƙwabta suka yi ƙoƙarin gaggawar kai ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Fatakwal (UPTH ) domin a ceto rayuwarta da ta abin da ke cikin cikinta, amma rai ya yi halinsa sakamakon munanan raunuka na sinadarin da saurayin ya watsa mata a jiki da ake zato sinadarin Asid ne.”
Kakakin ’yan sanda a Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa rundunar tana tsare da saurayin kuma yana bayar da haɗin kai a binciken da ke gudanarwa, kuma da zarar an kammala bincike, za a miƙa shi kotu ta yi aikinta.