✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zuwa ga Shugaba Muhammadu Buhari (4)

Saboda haka ya Shugabana! Lokaci ya yi da za ka samar da dawwamammen tsarin tattalin arzikin da zai sa talakawa farin ciki da annashuwa, kada…

Saboda haka ya Shugabana! Lokaci ya yi da za ka samar da dawwamammen tsarin tattalin arzikin da zai sa talakawa farin ciki da annashuwa, kada su kasance sun yi zaben-tumun-dare, sai safiya ta yi su rasa abin sa wa a bakin salati. Ka dai san irin halin kuncin da al’ummarka ke ciki, domin ka fada, ba sau daya ba, ba sau biyu ba, amma kullum na yi nazarin tsarin da kake bi na gudanar da tattalin arzikin kasa sai in ga tamkar madubin da kake amfani da shi, na duba-rudu ne, ko mai zagi, domin ni abin da nake hangowa, kai ba shi kake hangowa ba, ban sani ba, ko kai ba ka ji a jikinka ne, kamar yadda mu muke ji! Ga hujja!

Da hawanka mulki ya Shugaba! Ka bayyana mana cewa za ka cire tallafin da gwamnati ke bayarwa domin samar da albarkatun man fetur arha ko cikin rahusa ga al’ummar kasa, ta haka za a samar da fetur da kananzir da gas, yanfu-yanfu (wadace) a cikin kasa. Nan take ka ce ka ‘cire’ tallafin, wannan ne ya sa ka kara farashin fetur da kanazir da gas. Shi man fetur ka tada shi daga Naira 87 zuwa Naira 145, duk da cewa talakawa sun san karin farashin albarkatun man fetur zai wahalar da su, amma saboda imani da yarda da aminci da suke da shi game da kai, ga kuma dattakunka da rikon amana, da suke gani game da kai, suka hakura, suka mika wuya domin a yanka, in dai wannan shi ne zai kawo karshen matsalolin da ake fuskanta. Amma, ya Shugabana Buhari! Shin me ya canja daga shekara hudu da suka wuce zuwa yau?

Talakan Najeriya dai ya fahimci cewa shigo-shigo ba zurfi ne aka yi masa, domin kamar yadda jami’an gwamnatinka ke fada yanzu, bayan kusan shekara uku da cire tallafi, suna ikirarin wai ba a cire tallafin man fetur ba a can baya, yanzu ne ya kamata a cire. Wai, suna ce da mu abin da aka yi a baya shi ne ana dai biyan hamshakan ’yan kasuwa masu shigo da tataccen mai da Kamfanin NNPC, biliyoyin Naira na tallafi, domin a samar da albarkatun man fetur cikin sauki. Ya Shugabana! To ina amfanin karin kudin man fetur da aka yi a can baya, idan shi ba cire tallafi ba ne, me ya sa aka kara kudin man fetur da sauransu, shi kuma me sunan wannan tsari?

Shin yanzu in an cire tallafin, me zai faru, raguwar farashi ko kuwa karuwar farashi?  Me kai da gwamnatinka ke nufi da ake cewa za a cire tallafin ne a hankali, a hankali yanzu, ba irin da ba da ake cirewa, bagatatan?

Abin da nake da yakini shi ne kudin fetur da gas da kananzir karuwa za su sake yi da zarar ka cire ‘tallafin’ da ya rage. To ina amfanin badi ba rai!

Ba wannan kadai ba ya Shugaba Buhari! Shin ka taba tambayar kanka irin halin da talakawan kasar nan ke ciki dangane da tashin gwauron zabo da kayayyakin masarufi ke yi tun hawanka mulki, ba wai kawai fadar da kake yi na cewa ka san halin da ake ciki ba?

Na fadi haka ne domin na san ba kasuwa kake zuwa ba, ba ka kuma zuwa mahauta, ba ka kuma ziyartar dan tireda ko gyartai da mai gyaran takalmi ko mai yankar kumba. Haka ba ka shiga motar haya ko shatar ta daukar kaya daga gona. Haka kuma ba ka biyan kudin wutar lantarki ko sayen magani a kemis, bare uwa-uba kuma na san ba ka biyan kudin makarantar yara, bare kuma dinka musu kayan makaranta da na bukukuwan addini ko makamantan haka. Ba ka yin wadannan abubuwa a zahiri, domin wannan ai kuri’ar talaka ta raba ka da su, ta bar talakan da jangwam!

Haka kuma ya Shugabana! Na san kuma ba wani na kusa da kai, musamman iyalinka da ke ziyartar kasuwar talakawa domin su ji ko ganin yadda farashi ke tashin gwaurayen zabbi, balle su bayyana maka irin ‘ci gaban’ da aka samu a dan tsakanin da ka hau mulki zuwa yau. Ba sai na sake nanata maka ba, farashin man fetur da kananzir da gas, kusan ninkawa ka so a yi bisa ga farashin wanda ka gada daga gwamnatin baya. Saboda haka ina kira da ka samu lokaci ka leka cikin kowane gari ko kauye da kake bukata, ka tambayi al’umma ka ji halin da ake ciki. Ka samu lokaci ka yi hira kai-tsaye da wadansu daga cikin talakawanka, ka ji irin gararin da suke ciki. Shin ka san yadda suke ci da sha kuwa, ba wai irin ta-zo-mu-ji-tan da na kusa da kai ke fada maka ba?

Shin ka kuwa san cewa abincin ci, irin su shinkafa ko gero ko dawa ko masara ko wake ko alkama ko kuma mahadansu irin su gishiri ko daddawa ko magi ko madara ko kayan gwari, suna gagarar talakawa wajen yin abuta? Kuma dukkan wadannan sun yi tsallen-badake ba wai a zamanin tsohuwar gwamnatin Jonathan ba, a’a, daga hawan gwamnatinka zuwa yau da kake kan karagar mulki?

Ya Shugaba Buhari! Ya kamata ka yi nazari da kyau, ka kuma tambayi kanka ko ta canja zane a wasu sassan gudanar da mulkinka, musamman abin da ya shafi harkar ilimi da kiwon lafiya da tsaro a kasar nan? Shin ba ka san cewa gwamnatin da ka gada ta fi ka kassafa kudade domin inganta wadannan fannonin rayuwa ba, duk da kana cewa ka toshe hanyoyin sata da almundahana, ka kuma samar da asusun bai-daya da ya hana fitar da kudade ba tare da ka sani ba? Shin ina tarin kudin da aka ajiye? Me aka yi da su? Me ya sa abubuwa suka ki canjawa duk da matakan da ka bi na toshe kafafen barna? Abin da ya kamata ka tambayi kanka ke nan, kafin jama’a da tura ta kai bango su bayyana maka!

Za Mu Ci Gaba