✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zuwa ga [matashin] dan jarida

Ba yau aka fara wulakanta dan jarida ba a Najeriya ta hanyar kyara da kallon raini.

Tun [jiya] Asabar  na ga ’yan uwa ’yan jarida, da masu sha’awar aikin da abokan ’yan jarida na ta kumfar baki kan yadda aka nuna aikin jarida a shirin wasan kwaikwayo na Labarina da ake shiryawa a tashar Arewa 24. Bisa ga duk bayanan da na gani, mutane na nuna rashin jin dadin hantara da wulakanci da aka yiwa dan jarida a cikin shirin da kuma bashi kudin mota (brown envelope) da aka yi. Masu nuna rashin jin dadi na gani an ci mutuncin sana’armu. Amma meye bako a abin da aka nuna?

Ba yau aka fara wulakanta dan jarida ba a Najeriya ta hanyar kyara da kallon raini ko ma abinda ya zarta haka. Amma yadda wasu abokan aikinmu da yawa suka mayar da aikin shi ne yake jawo wannan wulakancin domin duk wanda ya maida kansa kaskantacce kuma mai kwadayi dole haka kowa zai gan shi kuma ya mu’amalance shi a haka. Wannan wulakanci kuwa yana da tushe, kuma yana da  alaka da yadda masu aikin da yawa suke shigarsa ba tare da sanin muhimmancin aikin ba ma.

Dan uwa, ka kuwa san cewa dan jarida yana da sahalewar tsarin mulkin Najeriya domin ya zama mai sa ido kan yadda duk sassan gwamnati ke gudunar da aikinsu don cigaban kasa? Wannan ne ya sa kamar alkali ko jami’in tsaro, ana sa ran dan jarida ya kasance mai gaskiya, da rashin tsoro, da kuma yin aiki ba-sani-ba-sabo domin dai tabbatar da fito da gaskiya da kuma sa wa masu mulki ido akan tabbatar da sun sauke hakkin jama’a da ke kansu. Kai wakilin jama’a ne kuma jama’a sun baka  amincewa shi yasa ma komai aka ji daga kafar yada labarai mutane kan amince da shi.

Don haka, wanda aka dorawa wannan babban nauyi ya kamata a ce an kula da shi ta fuskar albashi sannan shi kuma ya kauda kai daga kwadayin abin duniya. To amma a nan ne gizo yake sakar. Masu kafafen yada labarai da dama basu damu da sauke hakkin ma’aikatansu a kansu ba. Gidajen jarida da dama basa biyan albashi, ko kuma suna biyan abinda ko sati guda ba zai ishi mutum ba. Wasu kamfanonin da suka san muhimmancin kula da ma’aikata wurin yin aikin yadda ya kamata suna kokari sosai. Misali a kamfanin Daily Trust 25 ga wata ake biyan albashi. Haka nan a shekaru uku da wata biyar da na yi a Premium Times ba watan da ya taba karewa ba tare da an biya albashi, baya ga tsarin inshoran lafiya da fansho ga ma’aikata. Wannan sauke nauyi da kula da ma’aikata yana sa jajircewa da kuma rage hangen abin hannun wani.

Abu na biyu shi ne kwadayi. Saboda yanayin aikinmu, muna mu’amala da mutane masu hannu da shuni. Yawancinsu kuma suna da bukatarmu domin su gyara kansu ko kuma su bata wani, a don haka a shirye suke su “biya” domin bukatarsu ta biya. A irin wannan yanayi abubuwa biyu ne a gabanka: Tsayawa akan gaskiya da adalci (kamar yadda aikin ke bukata) ko kuma ka bi abin duniya.

Akwai wadanda za su baka kudi “na mota” ba tare da yarjejeniyar ga abinda lallai zaka yi musu ba. A haka zaka ga kamar bashi da illa amma yana da ita, babba ma kuwa. Idan ka je taro ko ka yi hira da wani aka baka kudi to ba makawa an siye ’yancinka na rubuta labari bisa yadda ya kamata domin kuwa ba zaka iya rubuta abinda ba zai yi wa wannan mutum dadi ba, koda kuwa shi ne abinda jama’a za su so sani. Kamar yadda Bahaushe ke cewa, idan baki ya ci, ido zai ji kunya.

Amma idan baka ci kudin mutum ba kana da ’yancin ka yi labarin ka yadda ka so, koma ka ki yi gaba daya. Bari in baka misali.

Kamar shekara uku da ta wuce akwai wani dan kasuwa da aka hada mu da shi, ni da Jaafar Jaafar akan cewa wani abokin kasuwancinsa ya cinye masa kudi. Mu ka hadu ya yi mana bayani dalla-dalla. Labari ne duk dan jarida zai so ya samu har ma da takarda na yadda aka turawa wancan babban dan kasuwa kudade. Da za mu rabu mutumin nan ya ce zai bamu kudi muka ce masa a’a. Ba yadda bai yi da mu ba amma muka ki. Har na fara rubutu labarin amma da muka samu ganin shi daya mutumin muka saurare shi sai take muka gane cewa wancan dayan gaskiyarsa bata cika ba, ya tauye bayanai kuma kawai yana son a kunyata wannan abokin harkar tasa ne. Muna fitowa muka yanke shawarar hakura da labarin, haka kuma muka bari. Da a ce mun karbi kudin wancan mutum na farko da watakila dole haka zai yi amfani da mu mu bata sunan wannan dayan duk da cewa shi wancan ba cikakkiyar gaskiya yake da ita ba. Shi yasa a kullum zaman lafiyarka a matsayinka na dan jarida shi ne gudun abin hannun mai baka labari (source).

Baya ga wadancan ginshikai guda biyu na san maganar ba dan jarida kudi tana kuma da nasaba da al’ada. Yawanci babba yana ganin abin kunya ne na kasa da shi ya hadu da shi bai bashi komai ba. Don haka ba wa dan jarida (wanda yawanci yaro ne matashi) “kuɗin mota” ya zama kamar karramawa ce irin ta al’ada, misalin irin wannan shi ne al’adar bada na goro ga ma’aikatan gidan abinci (restaurants) musamman a kasar Amurka. Su abin kunya ne ma ka ci abinci baka kara wani abu ba akan kudin abincin domin kyautatawa ga ma’aikata. Da na tambaya a wata tafiya da na yi US sai aka ce min suna saka “tip” ne saboda yawanci ma’aikatan ba a biyansu da kyau don haka abinda suka hada a hannun kwastoma da shi suke karawa a kan albashinsu. Amma kai da kanka na san zaka ce ai ba za a hada waiter na restaurant da kai da kake aikin bin bahasin mulkin jama’a ba. Sai dai kuma a daya hannun kamar yadda ma’aikacin gidan abinci a Amurka baya samun kyakkyawan biya, haka ma yawancin ma’aikatan jarida a Najeriya ga kuma bukatun rayuwa na yau da kullum. Idan haka ne, meye mafita? Akwai ta!

  1. Hada aikinka da wani abu: Samarwa kanka wata mashigar kudi musamman a bangarorin da ke da alaka da aikinka. Misali za ka iya gwanancewa a aikin fassara, ko bincike (research) ko bin diddigi (investigation/due diligence), ko bada horo (training) wanda wannan zai iya kawo maka kudi mai tsafta lokaci zuwa lokaci. Idan ka iya fassara kana zaune ma wani lokaci aiki zai fado. Misali bara a aikin fassara guda daya mun samu Naira miliyan biyu. Haka nan idan ka fara nisa a aikin zaka iya shiga sana’ar horar da ma’aikata wadda a lakca na awa daya kadai za a iya biyan ka daga N50,000 zuwa N200,000. Akwai kuma aikin jan ragamar taro (MC) ko daukar bayanan taro (rapporteur). Duk wadannan damarmaki ne da dan jarida zai iya sa kansa a ciki domin samun karin kudin shiga.
  1. Talla (adverts): Wasu gidajen jaridun su kan hana masu ainahin aikin rahoto shiga neman talla domin gudun hakan ma zai iya sa ɗan jarida ya zama baya iya tsage gaskiya kan wadanda suke bashi talla. Idan inda kake aiki basu da irin wannan matsayar, neman talla wata hanya ce da zaka iya samun karin kudaden kashewa domin kana da kamasho a duk aikin da ka kawo.
  1. Ƙulla alaka: Ka daure ka guji “biya” na nan take. Maimakon haka, yi kokarin kulla alaka ta mutunta juna. Yawanci duk masu ba da labarai (news makers) sun saba da cewa mu’amala da dan jarida sai ka tanadi kudi. Idan ka nuna kai na daban ne, nan da nan zaka jawa kanka mutunci da kuma mutuntawa. Maimakon kallonka a matsayin wani da aka haye shi domin ya yi aiki a biya shi, zai kalle ka a matsayin mutum. Da irin wannan halin sai ka ga Allah ya hada ka da mutumin da zaka amfane shi fiye da kudin da zai baka a wulakance, domin ita rayuwa ba komai ba ne kudi. Akwai abu da yawa da ya fi kuɗi wanda kuma mu’amala mai kyau ce kadai zata iya baka.

Akwai wani mutum da ya nemi kan wani labari mai zafi da yake son duniya ta sani. Da muka hadu bayan ya gama bani labarin sai ya ce zai bani takardu idan mun sake haduwa. Na same shi kuwa a gida amma da zai bani takardun sai cewa “Me zan samo maka to?” sai na ce “Kamar me?” Ya ce “Ah, abinda za ka rike mana don ka samu kwarin guiwar aiki” na ce masa “bana buƙatar komai”. Sai ya cewa ya yi gaskiya hankalinsa ba zai kwanta ya bani komai da komai ba idan bai bani kudi ba domin wadancan za su iya bani kudi mai yawa don kar a yi labarin. Sai na ce masa “Ai na ɗauka yarda ce ta sa ka neme ni. Idan baka yarda da ni ba to ma bari kawai”. Fadar mutumin yai ajiyar zuciya ya kawo documents ya bani. Na je na cigaba da aiki na yadda ya kamata. Wannan abin ya ja min mutunci kwarai a wajen mutumin nan kuma da wata bukata ta taso, ba tare da na roke shi ba haka ya bugi jikinsa da danyen kara ya yi min abin da ya ban mamaki. Wannan shi ne amfanin kulla alaka mai kyau.

Ya kai dan jarida, a karshen duk wannan batun ka sani kai ne babban alkalin kanka domin lokuta da dama da sanda za a nemi siye imaninka da mutuncinka daga kai sai mai baka kudin nan, sai Allah. A irin wannan yanayi conscience dinka shi ne linzamin ka. Aikin nan nauyin al’umma ne da amanarsu akan dukkaninmu. Ba kuwa babbar cin amana irin a hada baki da kai a fadawa mutane abinda ba haka ba, ko kuma ka zama karen farauta. Haka kuma duk mutumin da alakarku ta kasance ta “kuɗi hannu” ce ka tabbatar ba zaka taba yin kima a wurinsa ba. Zai kasance tsakaninka da shi sai yana da bukatarka idan ka zo ya “biya” ka ka yi masa abin da yake so. Shikenan.

Kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya fada: Ka guji abin hannun mutane, sai mutane su so ka.

Allah ya datar da mu.

Naka

Abdulaziz Abdulaziz