✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Finafinan Kannywood da suke tashe da kuma manyan marubutansu

Fitattun marubutan finafinan Kannywood da suke tashe.

Wani nazarin finafinan Kannywood da BBC Hausa ta gabatar ya nuna cewa, Masana’antar Kannywood tana ta samun sauye-sauye, musamman a bangaren shirya fim da kasuwancinsa, inda daga CD aka koma sinima, yanzu aka koma YouTube, sannan ake ta hankoron shiga manhajojin duniya ka’in da na’in.

A wannan shekarar, kamar kowace shekara, masu shirya finafinan Kannywood sun taka muhimmiyar rawa wajen tsarawa da fitar da finafinai masu kyau, wadanda suka kayatar da masu kallo.

Tun bayan komawa dora finafinai a YouTube, yanzu za a iya cewa harkokin Kannywood sun fara komawa yadda suke a baya, bayan a baya masana’antar ta fara durkushewa.

Nazarin ya yi tankaɗe da rairaye, sannan ya zakulo wasu finafinai da suke tashe. Sai dai kusan finafinan duka masu dogon zango ne, wanda hakan ke nuna yadda masana’antar ta sauya da kuma hanyar da ta dosa domin dorewarta.

Da farko da aka fara finafinai masu zango, an yi tunanin kananan masu shirya fim ne kawai suka yi, su ɗora a YouTube, har ma wasu suke ganin ba su da inganci.

Amma yanzu an wayi gari manyan furodusoshin Kannywood sun shiga ana damawa da su.

Daga cikin finafinan da aka zakulo, akwai wadanda an dade da fara yin su, amma har yanzu suna jan hankalin mutane. Ga yadda jerin finafinan ya kasance:

Labarina

Labarina fim ne mai dogon zango na fitaccen darakta, Malam Aminu Saira, wanda sunansa ya riga ya yi amo, ta yadda ba ya bukatar gabatarwa ga dukkan masu kallon finafinan Hausa.

Fim ne mai tsari shigen labarin ‘Dare dubu da daya’, inda daga wannan labarin za a shiga wani labarin daban, wanda a cewar daraktan, hakan zai sa fim din ya dade ba tare da ya salance ba saboda ba labari daya ba ne.

A shekarar 2020 aka fara fim din da labarin Sumayya wato Nafisa Abdullahi, wadda daga baya ta rikide ta koma Fati Washa, inda a karshen zango na bakwai aka dakata da labarin Sumayya, aka tafi hutu.

Amma yanzu labarin ya koma na Alhaji Mainasara wato Sadik Sani Sadik, wanda aka fara daga zango na takwas, kuma yanzu haka ana zango na 11.

Labari ne kan yadda Alhaji Mainasara ya batar da kama, ya fito a matsayin talaka domin samun soyayya ta gaskiya bayan wahalar da ya sha a farko, inda ya hadu da Jamila wato Amina Uba Hassan, ya nuna mata kauna.

Daga bisani ya tura mata direbansa da sunan yana da arziki, ita kuma ta amince da shi, maimakon Mainasara.

Ana cikin haka ita kuma kawarta, Maryam wato Fatima Hussaini ta amince za ta aure shi a haka.

Bayan aure komai ya fito fili. Amma daga baya matsala ta sa Maryam ba za ta haihu da shi ba, ta sa shi auren Dakta Asiya wato Diamond Zahra.

Fim din ya fitar da jarumai mata wadanda yanzu ake yi da su a masana’antar irin su Firdausi Yahaya da Fatima Hussaini da Amina Uba Hassan da sauransu.

Yawancin fitowar fim makomako na samu masu kallo sama da miliyan 1.

Manyan Mata

Fim din Manyan Mata shi ma ba a shekarar 2024 aka fara ba, amma yana ci gaba da jan masu kallo.

Fim ne da ya tara manyan jarumai masu yawan gaske, wanda za a iya cewa ba a saba ganin hakan ba.

Furodusa Abdul Amart Maikwashewa ne ya shirya, kuma ya dauki nauyi, sannan Sadik N. Mafia ya fara bayar da umarni, daga baya Ali Gumzak ya ci gaba.

A fim din an nuna yadda wasu mata suke shan wahala a gidajen miji da ’yan gudun hijira da sauran mata talakawa da yadda wasu suke amfani da damar da suke da ita wajen cin zarafinsu.

Sannan a gefe guda kuma, akwai mata biyu wato Laila (Hadiza Gabon) da Nadiya wato Aisha Tsamiya, wadda aka maye da Rabiatu Kafur da suke kokarin kwato ’yancin mata da kungiyarsu ta ‘Manyan Mata’, tare da kokarin nuna amfanin ilimin ’ya’ya mata.

Yanzu dai kallo ya koma sama, bayan rikici ya barke a tsakaninsu. Kusan duk wani babban jarumi a Kannywood yana cikin fim din, har da waɗanda aka daɗe ba a ji duriyarsu ba.

Yawancin fitowar fim ɗin a mako-mako yana samun masu kallo kusan 500,000.

Gidan Sarauta

Gidan Sarauta na cikin finafinai masu dogon zango na furodusa Abubakar Bashir Maishadda, wanda yake jan hankalin masu kallo.

An fara fitar da fim din ne a ranar 5 Nuwamban 2023 kuma jarumi Umar M. Shareef da jaruma Mommee Gombe ne suke jan fim din tare da taimakon Garzali Miko da Aisha Najamu.

Ali Nuhu da Hadizan Saima da Yakubu Mohammad da Rabiu Rikadawa da Abale duk suna cikin fim din.

An gina fim din ne a kan Umar M. Shareef, wanda ya fito a yarima mai jiran gado, ya fada soyayya da ‘yar talaka, Bintu (Momme Gombe), amma bai bayyana ba, daga kaninsa ya riga shi aurenta.

Amma sai aka gane akwai wani abu a tsakaninsu, wanda hakan ya sa kanin ya sake ta, shi kuma ya aura.

Wannan ya sa aka yi fushi da shi, aka ba shi zabin ko dai Bintu ko sarauta, inda ya zabi matarsa, ya hakura da sarautar.

Daga bisani shi ma Garzali ya hango yarinyar Tafida, wato Badariyya (Firdausi Yahaya), inda ya fada kogin kauna, amma yana tsoron shiga halin da yayansa yake ciki.

Ali Nuhu ne ya ba da umarnin a fim din, wanda dukkan jaruman suka dage wajen fitar da labarin fes.

Garwashi

Garwashi fim ne da aka fara fitarwa a ranar 12 ga watan Agustan 2024 a YouTube. An shirya fim ɗin ne a kan ƙalubalen da matan da mazajansu suka rasu suke fuskanta daga wurin ’yan’uwa da mutanen gari.

Jarumar shirin, Asma’u wato Firdausi Yahaya tana shan fama daga dangin mijinta da ’yan’uwanta da ma wuraren da take aiki.

Fitacciyar marubuciya Fauziyya D. Suleiman ce ta tsara labarin, sannan fitaccen darakta Yaseen Auwal ya ba da umarni.

Fim din ya dauki hankalin masu kallo sosai cikin kankanin lokaci, musamman ganin yadda jarumar take shan wahala.

Allura Cikin Ruwa

Fim ne da aka shirya kan Na’ima wato Rukky Ali, wadda marainiya ce, da aka tsinta bayan an harbe mahaifiyarta.

Daga baya maza irin su Maina wato Yakubu Mohammad, wanda take wa kallon kanin mahaifi da Alhaji Hadi wato Sani Danja da Dakta Hashim wato Adam A. Zango da Sadik wato Isa Ferozhkan, wanda suka daɗe suna soyayya, duk suka nuna sha’awar aurenta.

Daga baya an gano ashe tana da tarin dukiya da aka rasu aka bar mata. Saboda soyayyarta ce Maina ya fallasa cewa, Tijjani Faraga ba mahaifinta ba ne, don haka ya ce babu laifi don ya aure ta.

Kamfanin 2Effects ne ya ɗauki nauyin shirin, sannan Yakubu Mohammed ne ya ba da umarni.

Fitattun marubutan finafinan Kannywood da suke tashe

A harkar finafinan Hausa na Masana’anatr Kannywood, an fi mayar da hankali kan ‘yan fim din da suke fitowa, musamman ma wadanda suke jagorantar finafinan, inda akan manta da wadanda suke bayan fage.

A harkar, akwai masu ruwa da tsaki da dama da suke bayar da gudunmuwa wajen daukar fim, tun daga marubuta da masu fitilla da masu sauti da masu daukar bidiyo da tsara dandali da zirgazirga da sauransu.

A cikin wadanda suke aiki a bayan fage, an fi sanin furodusa da darakta, amma ba a cika ambaton sunan marubuta ba, wadanda kuma alkaliminsu ne yake saita fim, sannan idan ya samu aiki mai kyau, masu kallo su yaba.

Wannan ya sa muka rairayo wasu marubuta da alkalumansu suka rubuta finafinai wadanda suka yi shuhura, duk da cewa akwai zaratan marubuta da a ’yan kwanakin nan ba su yi wani aiki babba ba.

Yakubu M. Kumo

Yakubu M. Kumo, marubuci ne wanda a yanzu alkaminsa ke tashe a rubuce-rubucen finafinan Masana’antar Kannywood.

Daga cikin fitattun finafinan da ya rubuta akwai Labarina da Manyan Mata da Jamilun Jiddan da Gidan Sarauta da sauransu.

Ya dade yana rubuta finafinai masu inganci wadanda mutane suka yaba.

Fauziyya D. Suleiman

Fauziyya marubuciya ce da ta dade tana rubuta fitattun finafinai masu kayatarwa, tun daga kananan har zuwa masu dogon zango.

Daga cikin fitattun finafinan da ta rubuta akwai Dadin Kowa da take cikin marubutan fim din, wanda zuwa yanzu an kai shekara 10 ana yi.

A cikin finafinan da ta rubuta suke tashe, sun hada da fim din da yake tashe a yanzu wato Garwashi, kuma tana cikin masu shiryawa.

Mujahid Koguna

Mujahid Koguna da Yakubu Mohammad ne suka hadu wajen rubuta fim din Allura cikin ruwa na 2Effects kuma ya rubuta fim din Fansa.

Abdulkarim Papalaje

Abdulkarim Papalaje yana cikin sanannun marubuta kuma tsohon marubucin finafinan Hausa ne mai basira da yarubuta finafinai da dama da suka hada da Adamsy da Madubin Dubawa duka na Ali Nuhu da Ni da Matata da Oga Abuja da sauransu.

Nazir Adam Salihi

Nazir Adam Salihi shi ma sanannen marubuci ne da ya rubuta Gidan Badamasi.

Wasu marubutan da suka shahara sun hada da Jamil Nafseen da Nabila Rabi’u Zango da ya rubuta fim ɗin Umarni na furodusa Nazir Ɗanhajiya, waɗanda ana yabawa da su.