Gwamnatin Jihar Borno ta rushe gidaje 1,330 da aka gina a bakin gabar kogi a garin Maiduguri, don guje wa ambaliyar ruwa.
Hukumar Kula da Bayanan Muhalli ta Jihar Borno (BOGIS) ta fara aikin rusau din ne a kan Titin Bama zuwa Titin Damboa inda ta rushe gidaje da yawa.
- Abin da ya sa sojoji ba sa so yaki da ta’addanci ya kare —Sheikh Gumi
- Dole ce ta sa makiyaya suka fara amfani da AK-47 – Gwamnan Bauchi
- Dalibin aji hudu ya lashe gasar musabakar Al-Qur’ani a Kebbi
- Har yanzu El-Rufai bai fahimci batun matsalar rashin tsaro ba — Ganduje
A lokacin rusau din da ka yi a hanyar Damboa, Gwamna Babagana Zulum ya ce ko babu ambali zama kusa da kogi kasada ce.
Ya ce, “Mutane suna gini a kan hanyoyin ruwa kuma idan ba a yi komai ba za a samu ambaliya a babban birnin jihar, Maiduguri a lokacin damina.”
Zulum ya ce “tun shekarar da ta gabata” aka sanar da mutanen da aka rusa wa gidaje cewa su daina ayyukan gine-gine ko kuma su bar gidajen.
Ya ce duk kokarin da gwamnati ta yi don shawo kan mazauna da su daina gina gine-gine a wuraren da ba a ba da izini ba “ya gagara shi ya sa muka zo yau da safe don rusa duk wasu haramtattun gine-gine.”
Babban Sakataren BOGIS, Injiniya Adam Bababe wanda ya tabbatar da cewa an rusa gidaje kimanin 1,330 da aka gina a bakin gabar kogi ya ce an gudanar da aikin ne domin kauce wa barazanar ambaliyar a lokacin damina.