Gwamnan Babagana Umara Zulum ya rage farashin litar man fetur zuwa Naira 600 ga manoma a Jihar Borno.
Ya karya farashin ne ga manoman ƙananan hukumomin da rikicin Boko Haram ya addaba.
A yayin da gidajen mai ke sayar da litar fetur a kan N1,000 zuwa N1,200 a jihar Borno, Zulum ya bayyana ƙwarin gwiwa cewa ragin farashin zuwa N600 zai taimaka wajen haɓaka harkar noma da rage wa manoma kashe kuɗi.
Zulum ya bayyana cewa irin hakan da aka yi bara gamanoman Ƙananan Hukumomin Mobar da Damasak ya taimaka matuka wajen samun ƙaruwar abincin da aka noman.
Ya sanar da ragin farashin da kusan Naira ɗari huɗu ne a wurin rabon tallafin kayan noma ga manoma a 5,000 da suka dawo garuruwansu bayan hare-haren Boko Haram sun tilasta musu yin gudun hijira.
Kayan aikin gonan da ya raba wa manoma sun haɗar da buhunan takin zamani da iri da injinan ban-ruwa masu amfani da fetur da masu amfani hasken rana.
Ya ce gwamnatinsa ta ba da aikin gina rijiyoyin noman rani guda 250 domin bunƙasa noman rani a jihar.