Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi rabon tallafin kayan abinci ga ’yan gudun hijira da suka koma Karamar Hukumar Marte da zama.
Akalla mutum 2,870 ne suma koma cikin gidaje 500 da Gwamnatin Jihar Borno ta gina, kuma kowane magidanci a cikinsu ya karbi buhun shinkafa da buhun masara a rabon kayan tallafin na ranar Lahadi.
- Masu yi wa kasa hidima 25 sun kamu da COVID-15 a Gombe
- Makabartar Gombe da ake binne akalla jarirai 10 a kullum
Marte na daga cikin garuruwan da Boko Haram ta addaba, wanda ya sa mazauna yankin yin gudun hijra kafin daga baya sojoji su kwato garin.
Rukunin farko ke nan na wadanda suka koma garin, inda suka samu matsuguni a rukunin gidajen Hukumar Kula da Cigaban Yankin Yankin Tafkin Chadi (CBDA).
Galibin wadanda suka koma garin na Marte manoma ne, amma har yanzu ba su fara noma ba, ga shi damina ta jima da faduwa a Jihar ta Borno.
A lokacin ziyarar, Zulum ya tattauna hanyoyin da za a tallafa don inganta ayyukan noman rani don bunkasa rayuwar mutanen da suka koma garin, kamar yadda mashawarcinsa na musamman, Isa Gusau, ya bayyana.
Ya ce gwamnan ya kuma yi rangadin wata kasuwar wucin-gadi a garin na Marte inda ya ba da tabbacin tallafi daga gwamnati don bunkasa ayyukan tattalin arzikin mutanen garin.
Gwamnan ya kuma gana da kwamandojin sojoji game da tsaron mutanen da suka koma garin, tare da bukatar mazauna su ba wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai game da ayyukan da suka sabawa doka.
Sanata mai wakiltar Borno ta Arewa, Abubakar Kyari; da dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Marte da Manguno da kuma Nganzai, Mohammed Tahir Monguno; tare da Shugaban Ma’aikatan Jihar Borno, Farfesa Isa Hussaini Marte; da wasu kwamishinonin jihar na daga cikin wadanda suka yi wa gwamnan rakiya.