Gwamnan Borno, Bagabana Zulum, ya kaddamar da sabbin gidaje 100 da aka gina domin tsugunar da ’yan gudun hijira a Karamar Hukumar Gwoza ta jihar.
Da yake kaddamar da gidajen a madadin Gwamna Babagana Zulum, mataimakinsa, Usman Kadafur, ya yaba wa Gwamantin Tarayya da ta gina gidajen da nufin saukaka wa masu karamin karfi samun matsuguni.
- Yadda za a kawo karshen rikicin Rasha da Ukraine —Xi Jinping
- Za mu bullo da tsarin mafi karancin albashi a tamaula —UEFA
Ya ce gidajen da Gwamnatin Shugaba Buhari ta gina karkashin shirin samar da ci gaba mai dorewa (SDG) na Gwamnatin Tarayya za su kawo sauki ga mutanen Gwoza da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a yankin.
A jawabinta, hadimar Shugaban Kasa kan shirin SDG, ta ce an bullo da wani tsari mai wa’adin shekaru 25 ne a karkashin shirin da zummar samar da cigaba mai dorewa a Jihar Borno.
Ta bayyana cewa shirin samar da gidajen ya mayar da hankali ne kan mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.
Ta ce, “Zuwa shekarar 2030 ana sa ran jama’ar jihar Borno za su ci gaba da harkokin rayuwarsu yadda suke a baya kafin rikicin Boko Haram.”