Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa ya zabo Babagana Zulum ya gaje shi a jihar ne ba don kashin kansa ba sai dai don biyan bukatar jama’ar jihar Borno.
Kashim Shettima mai wakiltar jihar Borno ta tsakaiya a Majalisar Dattijai ya kara da cewa Zulum ya fi shi kwazo ta kowace fuska.
Tsohon Gwamnan Bornonn ya bayyana haka a yayin da yake gabatar da wata takarda a wani taro da gammayyar kungiyoyin matasa suka shirya a Birnin Kebbi mai taken “Rawar da jagororin Arewa za su taka wurin yi wa matasa jagoranci da bunkasa rayuwarsu”.
- A tarihin Najeriya babu shugaban da ya fi Buhari yaki da talauci – Lai Mohammed
- An kama matashin da ake zargi da kashe budurwarsa
- ‘Yan Kannywood sun yi tir da hotunan Rahama Sadau
Da yake magana game da Zulum, Shettima ya bayyana magajin nasa a matsayin dan siyasa mai gaskiya da amana.
Ya kuma shawarci shugabanni da su tuna cewa, mulki dai na Allah ne, yana da wa’adi kuma kowa sai ya yi bayanin abun da ya aikata a gobe kiyama.