Da safiyar ranar Laraba, Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya gabatar da cekin kudi na naira miliyan 20 ga iyalan da Marigayi Kanar Dahiru Chiroma Bako, kwamandan sojin da ya mutu sakamakon harin mayakan Boko Haram a Damboa.
Aminiya ta ruwaito cewa, Zulum yayin halartar jana’izar babban sojan a ranar Talata, 22 ga watan Satumba, ya yi alkawarin bai wa iyalan mamacin kyautar Naira miliyan 20 domin su ci gaba daukar nauyin kansu.
- Hotunan jana’izar kwamandan sojin Najeriya da Boko Haram ta kashe
- Zulum ya ba da N20m ga iyalan sojan da aka kashe
Gwamnan ya kuma ya sanar da cewa za a gina wa marayu da matar mamacin wadataccen gida duk inda suke so a fadin Najeriya domin su ci gaba da rayuwarsu a ciki.
“Na samu labarin cewa akwai sojoji uku da su ma suka rasa rayukansu tare da Kanar Bako, saboda haka, na ba da gudunmuwar kudi na naira miliyan biyu ga iyalan kowanne daga cikinsu”, inii Zulum.
Yayin da take karbar takardar cekin kudin, matar marigayi Kanar Bako, Rukayya Dahiru, ta yi godiya ga gwamnatin a bisa karamcin da ya yi musu.