✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Zulum ya bai wa dalibin da za a yi wa dashen koda tallafin N10m

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayar da tallafin Naira miliyan 10 ga wani dalibin jami’ar Maiduguri mai suna Mbahi Sarki Sulieman wanda…

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayar da tallafin Naira miliyan 10 ga wani dalibin jami’ar Maiduguri mai suna Mbahi Sarki Sulieman wanda za a yi wa tiyatar dashen koda.  

Mai magana da yawun gwamnan, Isa Gusau ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Dalibin mai shekaru 29 wanda ya fito daga Unguwar Yara ta Karamar Hukumar Hawul ya samu wanda zai ba shi kyautar kodarsa guda daya, amma ba shi da halin biyan kudin aikin dashen da za a yi masa a wani Asibiti da ke Abuja.

Hakan ya sanya ya kai kokensa a wani shiri na gidan Rediyo na Abuja inda ya nemi taimakon al’umma na kwarai a kan su tallafa masa da Naira miliyan 9 wanda ya ce ba ya da halinsu.

Bayan da wannan rahoto ya isa kunnen Gwamnan ne ya bayar da tallafin Naira miliyan 10 ga matashin a ranar Talata.

Isa Gusau ya ce gwamnan ya yi karin naira miliyan daya a kan kudin da matashin ya nema don watakila wata bukatar ta bazata na iya tasowa.

Mahaifiyar Matashin, Saratu Sarki Bitrus, ta ce tuni har sun biya kudin a Asibitin da za a yi wa danta dashen kodar a wannan mako.